Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan ƙwallo: Makomar Sancho, Torreira, Hudson-Odoi, Alli, Loftus-Cheek, Jorginho
A makon gobe Manchester United za ta yi tayin karshe inda za ta bayar da £90m don karbo Jadon Sancho daga Borussia Dortmund, in jiMirror.
Arsenal na son dauko dan wasan Chelsea da Italiya Jorginho, mai shekara 28. (Sky Sports - via Mail)
Dan wasanBarcelona da Brazil Philippe Coutinho, mai shekara 28, zai iya tafiya Arsenal domin zaman aro kafin a rufe kasuwar musayar 'yan kwallo. (Star)
Lucas Torreira yana dab da barin Arsenal, inda aka ce Atletico Madrid da Torino suna son dan wasan na Uruguay mai shekara, 24. (Independent)
Atletico Madrid na da kwarin gwiwar karbo aron Torreira, abin da zai sa Arsenal ta dauki dan wasan Madrid dan kasar Ghana Thomas Partey, mai shekara 27. (Sky Sports)
Alex Telles ya yi amannar cewa Manchester United ba za ta biya euro 20m (£18.3m) da Porto ta sanya a kansa kafin ta sake shi ba saboda a bazara mai zuwa dan wasan na Brazil mai shekara 27, yana iya barin kungiyar ba tare da an bayar da ko sisi ba. (Guardian)
Manchester City ta ce ikirarin da ta yi cewa sun taya dan wasan Atletico Madrid dan kasar Uruguay Jose Gimenez, mai shekara 25, a kan £78m ba gaskiya ba ne. (Goal)
Monaco ta bayyana sha'awarta ta dauko dan wasan Tottenhamdan kasar IngilaDele Alli, mai shekara 24. (90min)
Paris St-Germain na shirin janyewa daga tattaunawa don karbo aron Alli don yin kakar wasa daya. (Telegraph - subscription required)
Dan wasanChelsea da Ingila Callum Hudson-Odoi, mai shekara 19, yana son tafiya aro. (Talksport)
RB Leipzig na dab da dauko dan wasan baya abin da zai bai wa Dayot Upamecano damar barin kungiyar. Rahotanni masu karbi sun ce Manchester United na son dan wasan na Faransa mai shekara 21. (Star)