Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Dembele, Sancho, Alli, Aarons, Lingard, Milik

Ousmane Dembele

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United tana tattaunawa domin daukar dan wasan Faransa Ousmane Dembele, mai shekara 23, daga Barcelona, a cewar jaridar(Daily Record)

Sai dai (Mirror) ta ambato wasu majiyoyi a United suna yin watsi da alakanta kungiyar da Dembele.

Paris St-Germain na da kwarin gwiwar cewa dan wasan Tottenham Hotspur da Ingila Dele Alli, mai shekara 24, yana son zuwa wurinsu domin yin zaman aro na kakar wasa daya. (Mail)

Dan wasan Norwich City mai shekara 20 dan kasar Ingila Max Aarons ya amince da yarjejeniyar shekara biyar a Barcelona. (Sport - in Spanish)

Dan wasanArsenaldan kasar Faransa Matteo Guendouzi, mai shekara 21, ya mika bukatar barin kungiyar. (Tribal Football)

Borussia Dortmund ta dage cewa da wasan ngila Jadon Sancho, mai shekara 20, ba zai matsa ko'ina ba a lokacin musayar 'yan kwallo na bazara, duk da rahotanni masu karfi da ke alakanta shi da son tafiya Manchester United. (Independent)

Newcastle United na sha'awar dauko dan wasan Napoli da Poland Arkadiusz Milik, mai shekara 26. (Corriere dello Sport - in Italian)

Southampton wasan Ingila mai shekara 22 Tom Davies dagaEverton. (Talksport)

Arsenal za ta fuskanci hamayya daga kungiyoyin da ke buga gasar Zakarun Turai a yunkurinta na dauko dan wasan Lyon da Faransa Houssem Aouar, mai shekara 22. (Telegraph - subscription required)

Golan Argentina Sergio Romero, mai shekara 33, yana son barin Manchester United. (Sun)

Dan wasanChelsea dan kasar Jamus Antonio Rudiger, mai shekara 27, yana nazari kan makomarsa a kungiyar bayan da aka cire shi daga tawagar farko. (Sky Sports)