Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
FA Cup: Ba za buga wasan gida da waje ba a 2020/2021
Ba za a buga wasan gida da waje ba a gasar FA a kakar 2020-21 mai zuwa, "domin sassauta wahala" ga tsarin kwallon kafa.
Za a fara gasar da karin lokacin tun daga zagayen rukuni a ranar 1 ga watan Satumba a kuma buga wasan karshe a filin wasa na Wembley a ranar 15 ga watan Mayu, 2021.
Haka kuma an sanar da cewa wasan karabawo na kusa da na karshe za a buga shi ne sau daya.
An tsara buga zagayen farko na wasan a ranar 5 ga watan Satumba, yayin da sauran zagayen uku za a buga su a jere a lokacin wasannin tsakiyar mako a ranakun 15 da 16 ga watan.
An tsara za a fara gasar Premier ne a ranar 12 ga watan Satumba, yayin da za a buga zagayen karshe na wasannin a ranar 23 ga watan Mayun 2021. Hukumar gasar ta ce za a sanar da jadawalin kafin 21 ga watan Agusta.
Za a fitar da jadawalin 2020-21 na kakar wasannin ranar 21 ga watan Agusta tare da Championship. An kuma tsara fara Lig 1 da Lig 2 a ranar 12 ga watan Satumba.
Za a rika raba kyautar kudi da ake bayarwa ta kofin FA daga 2019-20 saboda matsalar tattalin arziki da korona ta haifar.
Wanda ya lashe gasar zai karbi fam miliyan 1.8 maimakon a baya da ake karbar fam miliyan 3.6, wanda hakan ya yi daidai da tsarin kakar 2017-18.
A ranar 18 ga watan Agusta za a kammala gasar FA da kofin kalubale.
Wasan karshe na kofin kalubale za a buga shi ne a Wembley a ranar 28 ga watan Fabirairu.