Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Thiago, Lacazette, Sarr, Grealish, Diawara, Pogba
Manchester City ta bi sahun kungiyoyin da ke fafutukar dauko dan wasan Bayern Munichdan kasarSufaniya Thiago Alcantara kuma an yi amannar cewa za ta biya fiye da kudin da Liverpool ta ware don dauko dan wasan mai shekara 29. (SportBild - via Star)
Manchester United ta dakatar da sauran shirye-shiryenta na musayar 'yan kwallo a yayin da take kokarin dauko dan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jadon Sancho, dan shekara 20. (Mirror)
Juventus ta tuntubiArsenal kan yiwuwar musayar dan kwallon Faransa Alexandre Lacazette, mai shekara 29. (CalcioMercato - in Italian)
Watford za ta bukaci a biya ta £40m kan dan wasan Senegal Ismaila Sarr, mai shekara 22, a yayin da Liverpool da wasu kungiyoyin Turai ke zawarcinsa. (Evening Standard)
Sarr ya shaida wa manema labarai cewa a kasarsa "kowa yana so" ya buga tamaula a Liverpool. (Sans Limites - via Goal)
Roma za ta iya musayardan wasan Guinea mai shekara 23 Amadou Diawara da dan wasan Arsenal dan kasar Uruguay Lucas Torreira, mai shekara 24. (Gazzetta dello Sport - via Mail)
Jack Grealish zai tattauna da shugaban Aston Villa Christian Purslow idan ya koma daga hutun da yake yi, a yayin da har yanzu Manchester United take ci gaba da nuna sha'awar dauko dan wasan mai shekara 24. (Mirror)
Benfica na kan gaba a yunkurin dauko tsohon dan wasan Tottenham Jan Vertonghen kuma mai yiwuwa dan wasan mai shekara 33 dan kasar Belgium zai iya yin aiki tare da tsohon dan wasan Paris St-Germain Edinson Cavani, mai shekara 33. (Sun)
Daraktan wasanni naLyon Juninho ya bayyana cewa dan wasan tsakiya Houssem Aouar zai iya barin kungiyar a bazara, a yayin da Arsenal, Manchester City da Juventus suke sanya ido kan dan kasar ta Faransa mai shekara 22. (Mail)
Dan wasan tsakiyar Faransa Paul Pogba, mai shekara 27, yana sa raiManchester United za ta soma tattaunawa da shi da zarar an kammala gasar Europa League. (Sky Sports)
Arsenal tana matukar son dauko dan wasan Sporting Lisbon dan shekara 17 Joelson Fernandes. Ana yi wa dan wasan lakabi da 'sabon Cristiano Ronaldo' kuma mai yiwuwa Arsenal ta bayar da kudi da 'yan wasan domin dauko shi. (Mirror)
West Bromwich Albion da Fulham suna fafatawa don dauko dan wasanPeterborough dan kasar Ingila Ivan Toney, mai shekara 24. (Football Insider)
Tottenham ta amince ta kyale dan wasan Ingila dan shekara 19 Oliver Skipp da takwaransa Jamie Bowden su tafi zaman aro bayan ta dauko Dane Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 25,Southampton. (Football Insider)
Atletico Madrid tana son dauko golan Eibar dan kasar Serbia Marko Dmitrovic, mai shekara 28, domin ya maye gurbin dan wasan Slovenia Jan Oblak, mai shekara 27, wanda ake rade radin zai tafi Chelsea. (Goal)