Dortmund ta ce Sancho ba na sayar wa ba ne

Dan wasan Ingila Jadon Sancho zai ci gaba da zama a Borrusia Dortmund har zuwa kaka ta gaba, in ji daraktan wasannin kungiyar Micheal Zorc.

An sanya sunan dan wasan mai shekara 20 cikin jerin wadanda za su yi atisaye a sansanin kungiyar da ke Switzerland.

Wannan na zuwa ne a daidai ranar da kungiyar ta tsayar domin kammala cinikin Sancho, wanda shi ne babban dan wasan da Manchester United ta sanya a gaba a wannan kakar.

"Mun gina kungiyarmu da Sancho a wannan kakar," in ji Zorc.

"Wannan kuma ita ce matsayarmu ta karshe. Ina kuma ganin hakan zai amsa dukan tambayoyinku."

"A bara muka kara masa albashi domin ya yi daidai da kokarin da yake. Don haka, a fakaice mun kara kwantaraginsa ne zuwa 2023."

Kungiyar da ke buga Bundesliga na neman fam miliyan 100 ne kan dan wasan na Ingila, wanda suka dauko daga Manchester City a 2017 kan kudi fam miliyan 10.

Kungiyar dai ta tsayar da lokacin da ta ke bukata a kammala wannan cikinki tsakaninta da United, saboda ta mayar da hankali kan shirye-shiryen sabuwar kakar da za a shiga ta 2021 da 2022.

Za a fara sabuwar kakar wasanni a Budesliga a ranar 18 ga watan Satumbar gobe, yayin da za a rufe kasuwar musayar 'yan wasa a ranar 5 ga watan Oktoba.