Premier League: Southampton ta sayi ɗan ƙasar Ghana

Southampton ta dauki dan bayan kasar Ghana Muhammed Salisu daga Real Valladolid kan kudi fan miliyan 10.9.

Dan wasan mai shekara 21, wanda ya buga wasa 32 a kungiyar ta Spaniya a kakar da aka kammala, ya sanya hannu kan kwantaragin shekara hudu ne.

Kocin kungiyar ta Southampton ya ce " Wannan ciniki ne mai mahimmanci gare mu, Muhammed dan wasa ne mai lafiya da zai dace da kungiyarmu."

A wannan makon ne Saint ta kammala daukar dan wasan bayan bayan Tottenham kyle Walker Peter kan kudi kimanin fam miliyan 12.

Salisu ya ce: "Southampton babbar kungiya ce mai tarihin fitar da matasan 'yan wasa, dan haka ya yi dai-dai da ni ta yadda zan iya bunkasa kwarewata in kuma koyi abubuwa da dama a matsayina na matashin dan kwallo."