Champions Leagu: Dan wasan Barcelona ya kamu da korona

Barcelona ta ce daya daga cikin 'yan wasanta da ba ta bayyana sunansa ba ya kamu da cutar korona.

Yana daya daga cikin 'yan wasa tara da suka halarci atisaye gabanin fara sabuwar kaka, bai dai nuna ko alama daya ba ta masu cutar, kuma har an killace shi a gidansa.

Barca ta ce dan wasan bai yi mu'amala da ko daya daga cikin manyan 'yan wasanta ba, wadanda za su je Lisbon ranar Alhamis domin shirin wasansu na gasar zakarun turai.

Ita ma Valencia ta tabbatar da mutum biyu da suka kamu da wannan cuta cikin 'yan wasanta a wannan makon, haka zalika Atletico Madrid ta ba da rahoton samun mutum biyu cikin tawagarta gabanin wasan da za su buga na kusa da daf da na karshe a Champions.

Saboda annobar korona, za a ƙarasa gasar Champions a Lisbon, kuma ko wanne wasa za a buga shi sau daya ne kamar wasan karshe ba tare da 'yan kallo ba.

Barcelona za ta kara da Bayern Munich kwana daya bayan Atletico ta barje gumi da RB Leipzig.

Dukkan mutanen da aka ga sun yi mu'amala da 'yan wasan Barcelona ana bibiyarsu ana yi musu gwaji.