Jimenez zai tafi Manchester United, Gareth Bale zai ci gaba da zama a Real Madrid

Dan wasan gaban Mexico Raul Jimenez, mai shekara 29, yana kan hanayarsa ta zuwa Manchester United bayan Wolves ta amince d yarjejeniyar £27m domin dauko dan wasan Braga dan kasar Portugal mai shekara 27 Paulinho. (RTP, via Express)

Tsammanin da ake yi wa Jadon Sancho na tafiya Manchester United ya matso kusa, a yayin da Borussia Dortmund ta ce za ta yarda da tayin farko na £60m da aka yi mata kan dan wasan na Ingila mai shekara 20. (Independent)

Chelsea ta gabatar da bukatarta ta dauko golan Barcelona dan kasar Jamus mai shekara 28 Marc-Andre ter Stegen. (Cadena Ser, via Mail)

Gareth Bale, mai shekara 31, ya shaida wa kocin Wales Ryan Giggs cewa ya yanke shawarar ci gaba da zama a Real Madrid a kakar wasan badi duk da yake rashin sanya shi a wasa ya sa ba ya samun kudi. (Mirror)

Chelsea da Manchester City na cikin manyan kungiyoyi da ke sanya ido kan dan wasan Austria David Alaba, mai shekara 28, don ganin ko zai sabunta kwangilarsa a Bayern Munich. (Telegraph)

Leeds na shirin dauko 'yan wasa biyu - dan wasanEverton Fabian Delph, mai shekara 30, da kuma dan wasanTottenham Danny Rose, mai shekara 30 - a yayin da kocin kungiyar Marcelo Bielsa yake son 'yan wasan da suka kware a Gasar Firimiya. (Star)

Golan Argentina Sergio Romero, mai shekara 33, yana son tattaunawa da Manchester United game da makomarsa - a yayin da golan Ingila Dean Henderson, mai shekara 23, ya kama hanyarsa ta komawa Old Trafford bayan zaman aron da ya yi a Sheffield United. (Sun)

Ana sa rai Inter Milan za ta amince da yarjejeniyar sayen dan wasan Chile Alexis Sanchez, mai shekara 31, daga Manchester United a bazarar nan. (Manchester Evening News)

Har yanzuSouthampton tana jiraTottenham ta sayi dan wasan Denmark mai shekara 24 Pierre-Emile Hojbjerg a farashin da ya dace. (Daily Echo)

Mesut Ozil, mai shekara 31, zai ci gaba da zama a Arsenal a bazarar nan yayin da wakilinsa ya ce tsohon dan wasan na Jamus yana so ya ci gaba da zama har lokacin da kwangilarsa za ta kare a Emirates Stadium. (Mail)

Liverpool na shirin dauko dan wasan Bournemouth Lloyd Kelly, mai shekara 21, bayan da suka gaza dauko shi wata 12 da suka wuce lokacin yana Bristol City. (Express)

Kazalika kocinLiverpool Jurgen Klopp zai yanke shawara kan dan wasan Ingila mai shekara 20 Rhian Brewster bayan ya kammala zaman aro a Swansea. (Liverpool Echo)