Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ndubisi Egbo: Kocin ƙwallo ɗan Najeriya da ya kafa tarihi a Albania
Ɗan Afirka na farko da ya taɓa kai wata ƙungiyar kwallon ƙafa ta Turai zuwa gasar Zakarun Turai, mai suna Ndubisi Egbo na ƙungiyar KF Tirana ta ƙasar Albania ya bayyana irin cin mutunci da cin fuskar da ya fuskanta a kakar wasa ta bana a kan hanyarsa ta kafa tarihi.
A ƙarshen makon jiya aka tabbatar wa KF Tirana matsayinta na zakarun lig ɗin Kategoria Superiore wanda shi ne ƙololiyar matakin gasar kwallon kafa ta maza a Albania.
Wannan namijin ƙoƙarin da kocin yayi zai ƙara bayar da sha'awa idan aka yi la'akari da cewa a tsakiyar kakar wasan ya karɓi ragamar ƙungiyar, a lokacin tana fuskantar barazanar mayar da ita aji na baya na gasar ƙwallon ƙafar ƙasar.
Amma tsohon mai tsaron gidan na ƙungiyar Super Eagles ta Najeriya - wanda ke riƙe da fasfon Najeriya da na Albania - ya koka da yadda aka riƙa nuna ma sa bambancin launin fata.
"Akwai mutane da dama da ba sa son in yi nasara saboda launin fata ta," inji kocin mai shekara 47 da haihuwa.
"Akwai matsalar nuna bambancin launin fata. A yayin wani wasa sun jefe ni da ayaba. Sun tofa min miyau."
"Shuganannin hukumar kwallon ƙafa ta Albania ba su ɗauki wani mataki ba saboda mun je gidan wata ƙungiya ce wasa, kuma magoya bayansu fararen fata ne."
"Ƴan sanda da sauran jami'an tsaro na wurin - amma babu wanda yayi wani abu a kan lamarin. Suna tsoron magoya bayan ƙungiyar a can. Ban iya yin komai ba. Haka na haƙura."
Egbo ya kuma bayyana cewa ya kan ji ana zunɗe a kansa domin sun ɗauka baya jin yaren Albania.
Akwai ranar da ya ke ƙoƙarin shiga wata motar haya ɗauke da jakarsa, sai ya ji wasu mutum biyu a bayansa suna cewa da Albaniyanci "wannan daga gani ɗan Al Qaeda ne."
"Sai na ce mu su, 'kun gama'?" da Albaniyanci - yaren da ya ƙware matuƙa kansa.
"Sun ji kunya kamar ƙasa ta tsage su shige cikinta."
'Kamar Obama'
Egbo ya taɓa riƙe mukamin mataimakin kocin ƙungiyar bayan da ya koma ƙasar a matsayin mai tsaron gida kuma kocin masu tsaron gida a 2014, ya kama aiki gadan-gadan bayan da aka kori tsohon manajan ƙungiyar a karshen 2019, a lokacin Tirana na mataki na takwas a teburin gasar da ke da ƙungiyoyin ƙwallo 10 kawai.
"Muna cikin mawuyacin hali, domin muna ganin da ƙyar za mu kai labari," inji shi.
"Akwai tazarar maki fiye da 15 tsakaninmu da ƙungiyar da ke saman teburi. Amma cikin wasanni 23 da muka buga, mun lashe 20. Sai wanda ya san halin da muka shiga ne zai iya sanin wahalar da muka sha."
Ya ce koci-koci baƙar fata da yawa sun kira shi suna jinjina ma sa bayan kafa tarihin da yayi a ƙarshen makon jiya.
"Ƴan uwana ƴan Afirka sun ce, 'ba ka san martabar da ka janyo mana ba da ka lashe wannan gasar'," inji shi.
"Wannan yayi kama da lokacin da Obama ya lashe zaɓen shugaban Amurka. Haka ake kallon lamarin a nan."
Amma ya ƙara da cewa, duk da yayi farin cikin "kafa tarihi" kan yadda ake kallon masu horar da ƴan wasa ƴan Afirka, akwai jan aikin da ya kamata a yi domin sauya halayyar mutane.
Ya ce ya lura da halin da tsofaffin ƴan wasa ke shiga bayan sun daina buga ƙwallo a Ingila - inda lamarin ya bambanta idan ɗan ƙwallon baƙar fata ne ko bature ne.
Ya ce: "Idan ka kalli gasar firimiyar Ingila, da wuya ka sami koci baƙar fata a can."
"Lamarin na sani jin daɗi a wani lokaci, amma na kan shiga damuwa a wani lokacin na daban."
Ya ce ba a ba baƙaƙen fata dama kamar ƴan uwansu farar fata, "Mu ma muna buƙatar a bamu irin damar da ake ba su."
"Wannan tamkar batun nan ne da ake yaƙi da launin fata na Black Lives Matter, wato Rayuwar Baƙar Fata na da Ƙima, amma a fagen wasan ƙwallon ƙafa ya kamata mu ma a bamu dama".
KF Tirana za ta fara buga gasar Zakarun Turai, amma sai ta lashe wasanni huɗu idan tana son karawa da manyan ƙungiyoyin Turai.