Nathan Ake: Manchester City ta sayi dan wasan Bournemouth kan £40m

Kungiyar kwallon kafar Bournemouth ta amince ta sayar wa Manchester City dan wasanta Nathan Ake a kan £40m.

Dan wasan dan kasar Netherlands, mai shekara 25, ya tafi Bournemouth ne a 2017 kuma ya buga mata wasa 121 inda ya ci kwallo 11.

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya dade yana son dauko Ake.

An fitar da Bournemouth daga gasar Frimiya bayan ta gama kakar bana a matsayi na 18, yayin da ita kiuma Manchester City ta kammala kakar a matsayi na biyu.

An fahimci cewa Ake zai bar Bournemouth a bazarar nan ko da kuwa sun taka rawar gani ko akasin haka.

Don haka, fitar da su daga Firimiya ya karfafa gwiwar City wajen soma tattaunawa da shi.