Vertonghen da Pedro sun kara gaba

Dan kwallon Tottenham, Jan Vertonghen zai bar kungiyar bayan shafe shekaru takwas tare da kulob din.

Vertonghen dan shekaru 33, ya buga wasanni 315 a Tottenham amma bai samu dama ba sosai a karkashin sabon kocinsu Jose Mourinho.

Dan kasar Belgium din a yanzu yana neman kulob bayan da a bara ya taimakawa Spurs ta kai wasan karshe na gasar zakarun Turai da kuma gasar League ta Ingila.

Dan kwallon Spaniya, Pedro ya buga wa Chelsea wasa na karshe a ranar Lahadi kamar yadda kocinsa Frank Lampard ya tabbatar.

Pedro mai shekaru 33, ya koma Chelsea ne daga Barcelona a kan fan miliyan 21 a shekara ta 2014, sannan ya taimakawa Chelsea ta lashe gasar Premier a shekarar 2017 da kuma gasar kofin FA da kuma Europa.

Rahotanni sun nuna cewa zai taka leda a AS Roma.