Tottenham: Ban damu da kora ba - Pochettino

Kocin Tottenham Mauricio Pochettino ya ce ba shi da wata damuwa game da rade-radin korarsa daga aiki duk da rashin kokarin da kungiyarsa take yi a 'yan kwanakin nan.

Spurs ta yi rashin nasara da 3-0 a Brighton ranar Asabar biyo bayan wani shan kashin da ta yi cikin mako guda da ci 2-7 a hannun Bayern Munich a gasar Champions League.

Kazalika an cire kulob din daga gasar Carabao Cup a bugun finareti a watan da ya gabata, inda Colchester, mai buga gasar League Two, ta yi waje rod da ita.

Da aka tambaye shi ko yana jin wata damuwa game da aikinsa, Pochettino ya ce: "Sam ban damu ba, abin da ke damu na ita ce rayuwa, ba kwallon kafa ba."

Da yake magana a wajen wani taron manema labarai bayan wasan na jiya Asabar, Pochettino ya kara da cewa: "Wata rana ka yi nasara a kwallon kafa wata rana kuma ka sha kashi.

"Mu matsalarmu ita ce kawai nasara, nasara, nasara kuma haka ake ta yabon kowa da kowa.

"Amma a wasa biyu da suka gabata kowa ya ji a jikinsa. Sai dai ba na son yin maganar da ba ta dace ba ko kuma dadin baki."

"Za mu kawo karshen matsalar"

Rashin nasarar ta baya-bayan nan tana nufin Tottenham, wadda ke buga Champions League, ta samu maki 11 daga wasa 24 a wannan kakar kuma ta gaza cin wasa ko daya cikin 10 na waje a Premier.

Wasan karshe da ta ci shi ne wanda ta ci Fulham 2-1 ranar 20 ga watan Janairu.

Baki daya ta yi rashin nasara a wasa 17 a dukkanin gasa a 2019 - sama da kowacce kungiya mai buga babbar gasa a Ingila.

Kazalika, abin ya kara ta'azzara ne saboda rashin tabbas na wasu manyan taurarin 'yan wasanta - Eriksen da Vertonghen da Alderweireld duka suna shekarun karshe na kwantaraginsu.

"Kwallon kafa baki dayanta ta danganci jajircewa ne da kuma daukar matakai sannan kuma idan abubuwa ba su tafi yadda ya kamata ba kada ka buya," in ji Pochettino.

"Abin da za mu yi kenan, mu kawo karshen matsalolin sannan mu kokarta wajen sauya tafiyar.

"Wajibi ne in dauki alhakin duk abin da ya faru kamar yadda nake jin dadi idan aka yabe ni ko kuma kungiyar."

Pochettino ya fara aikin horar da Tottenham a 2014.

Sakamakon wasannin Premier Asabar:

Wasannin Lahadi: