Premier League: Liverpool ta ci wasa da kyar

Bugun finareti na mintin karshe da James Milner ya ci ne ya bai wa Liverpool nasararta a kan Leicester City mai cike da hatsaniya a wasan mako na takwas a filin wasa na Anfield.

Tawagar Brendan Rodgers ta nuna da gaske take lokacin da James Maddison ya farke kwallo ana saura minti 10 a tashi, wadda Sadio Mane ya zura masu a raga a minti na 40.

Ita ce kwallo ta 50 da Sadio Mane ya ci a gasar Premier.

Sai kuma bayan an shiga mintunan karshe ne Marc Albrighton ya kayar da Mane a cikin yadi na 18.

Bayan tattaunawa da mataimakan alkalin wasa, masu kula da na'urar VAR, aka bayar da bugun finaretin kuma bayan Milner ya ci aka ga koci Jurgen Klopp yana murna, inda shi kuma Rodgers ya fita daga fili cikin alhini.

Kazalika dan wasa Ayoze Perez na Leicester City ya so ya yi hatsaniya da wasu 'yan wasan Liverpool wadancda suke murnar cin wannan wasa.

Wannan shi ne wasan da ya fi bai wa Liverpool wahala a Premier ta bana, inda ta kusa sha kashi a wasan.

Yanzu haka maki takwas ta bai wa Manchester City, wacce ke mataki na biyu.

Sai dai Man City za ta iya rage yawan makin idan ta ci wasanta da Wolves ranar Lahadi da karfe 2:00 agogon Najeriya da Nijar.