Premier League: Tottenham ta sake shan kashi

Tottenham ta ci gaba da shiga tasku kari a kan wanda Bayern Munich ta saka ta bayan Brighton ta ragargaje ta da ci 3-0 a wasan Premier mako na takwas.

Bayan 7-2 da aka ci su a tsakiyar makon jiya, Tottenham da Pochettino sun tsammaci farfadowa amma sai mai tsaron raga Hugo Lloris ya bai wa Brighton kyautar kwallonta ta farko.

Kyaftin din Tottenham din ya ji rauni a hannunsa saboda kwallon da ta subuce daga hannunsa, inda shi kuma Aaron Connolly ya jefa ta raga kafin ya ya kara ta biyu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Connolly dan kasar Ireland mai shekara 19, ya jefa ta biyun wadda ta bai wa Brighton nasararta ta farko a gida a wannan kakar.

Yanzu Tottenham ta yi wasa 10 a waje ba tare da nasara ba a Premier - rabonta da nasara tun Janairu inda ta ci Fulham 2-1.

Kuma tana matsayi na bakwai da maki 11.