Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal ta daukaka kara kan jan katin da aka yi wa Nketiah
Arsenal ta daukaka kara kan jan katin da aka yi wa dan wasanta Eddie Nketiah wanda aka kora a karawar Premier ranar Talata a wasa da Leicester City.
Tun farko an bai wa Nketiah mai shekara 21 katin gargadi kan ketar da ya yi wa mai tsaron bayan Leicester City, James Justin.
Daga baya aka sauya hukuncin zuwa jan kati, bayan da alkalin wasa Chriss Kavanagh ya tuntubi na'urar da ke taimakawa alkalin wasa yanke hukunci wato VAR ya sake kallon abinda ya faru.
An dakatar da Nketiah wasa uku za kuma a sanar da hukuncin kafin wasan da Arsenal za ta yi da Tottenham ranar 12 ga watan Yuli.
Gunners za ta karbi bakuncin wacce ta lashe kofin Premier League na bana wato Liverpool daga nan ta fafata da Manchester City a karawar daf da karshe a FA Cup.
Wani kwamiti ne mai zaman kansa zai saurari daukaka karar jan katin Nketiah, za kuma a kara yawan kwanakin hukuncin idan an kara samun dan wasan da laifi.