Solskjaer na son Pogba ya tsawaita yarjejeniyar zama a Old Trafford

Kocin Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer na son Paul Pogba ya sa hannu kan doguwar yarjejeniyar da zai ci gaba da taka leda a Manchester United.

Kafin bullar cutar korona, alamu sun nuna cewar dan wasan tawagar Faransa na shirin barin Old Trafford da an kammala kakar bana.

An yi ta alakanta dan kwallon mai shekara 27 da cewar zai koma tsohuwar kungiyarsa Juventus ko kuma Real Madrid.

Sai dai kuma bayan da Pogba ya warke daga jinya ya ci gaba da buga wasa, inda kwallonsa ke kyau da Bruno Fernandes a kokarin da kungiyar ke yi a neman gurbin Champions League na badi.

Kwantiragin Pogba zai kare a Old Trafford nan da wata 12, sai dai kuma United tana da zabin tsawaita zamansa a kungiyar zuwa kaka daya.

Bayan da Nemanja Matic da Scott McTominay suka amince su ci gaba da wasa a United, Solskjaer na kuma son Pogba wanda ya yi fama da rauni a bana da ya ci gaba da zama a kungiyar.

Ana sa ran Solskjaer zai sayo karin 'yan kwallo a bana ciki har da dan wasan Borussia Dortmund, Jadon Sancho da wasu da ya dade yana bibiyar kwallon kafar da suke yi.