Man City ta ragargaji Newcastle United a Premier

Manchester City ta ragargaji Newcastle United da ci 5-0 a gasar Premier League da suka fafata a Etihad ranar Laraba.

Kungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama ta sha kashi a hannun Southampton a wasan baya da ta buga, amma nan da nan ta zura kwallo biyu a ragar Newcastle tun kan hutu.

Gebriel Jesus ne ya fara cin ta farko, ya kuma kawo karshen wasa tara bai zura kwallo a raga ba, bayan da David Silver ya ba shi tamaula, sai Maharez da ya ci wa City na biyu.

Bayan da suka yi hutu suka kuma koma zagaye na biyu ne, abubuwa suka kara balbalce wa Newcastle da ta kai cin kanta da kanta ta hannun Federico Fernandez.

David Silva ne ya ci wa City kwallo na hudu, yayin da Raheem Streling wanda ya shiga karawar daga baya ya kara na biyar a raga a cikin karin lokaci kan tashi daga fafatawar.

Saura wasa hurhudu a karkare gasar Premier League ta shekarar nan, City ta jaddada zamanta a mataki na biyu a kan teburi da tazarar maki tara tsakaninta da Chelsea.

Ita kuwa Newcastle United ta yi kasa zuwa mataki na 13 a kasan teburin Premier League na bana.

Tuni dai Liverpool ta lashe kofin gasar Premier League na 2019/20, kuma na farko tun bayan shekara 30 na 19 jumulla.