Modric ya yi wasa na 150 da Madrid ta ci a La Liga

lUCA mODRIC

Asalin hoton, Real Madrid FC

Ranar Lahadi Real Madrid ta dare kan teburin La Liga, bayan da ta doke Real Sociedad da ci 2-1, karo na 150 da Modric ya buga fafatawar da aka yi nasara da ci.

Real da Barcelona suna da maki iri daya, amma karawar da Madrid ta yi nasara a El Clasico ne ya sa ta koma ta daya a teburin.

Luca Modric ya buga karawar a gidan Sociedad wanda ya canji Marcelo kuma wasa na 150 kenan da ya yi wa Madrid a La Liga da aka samu nasara da shi.

Jumulla dan kwallon tawagar Croatia ya yi wa Real wasa 225 ya kuma ci kwallo 15.

Kakar da ya fi taka rawar gani ita ce ta 2012-13 da ta 2013-14 inda yana daga cikin 'yan wasan da Real ta ci karawa 24.

A kakar bana kuwa ya buga gasar La Liga karo 24 an kuma yi nasara a fafatawa 16 tare da shi.

Ya kuma ci kwallo kwallo uku a wasa da Real Sociedad da Granada da kuma Getafe.

Modric ya lashe Champions League hudu da kofin zakarun nahiyoyi wato Club World Cups.

Haka kuma da shi Real Madrid ta dauki UEFA Super Cups uku da na La Liga da Copa del Rey da kuma Spanish Super Cups uku.