Coronavirus: Man United ta ce ta yi asarar fam miliyan 28 kawo yanzu

Old Trafford

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Manchester United tana mataki na biyar a kan teburin Premier a lokacin da aka dakatar da wasanni saboda bullar cutar korona

Manchester United ta ce bullar cutar korona ta jawo mata hasarar fam miliyan 28 - tana kuma fargabar hasarar za ta fi haka nan gaba.

United ta sanar da kasuwancin da ta yi na zango na uku ranar Alhamis 30 ga watan Maris.

Jami'in kudi na United, Cliff Baty ya ce sun shirya mayar da fam miliyan 20, kudin tallata wasa a talabijin ko da an kammala wasannin bana.

United ta yi hasarar karin fam miliyan takwas a mako uku na cikin watan Maris, bayan da aka dakatar da wasanninta uku.

Wasannin United 11 jumulla aka dakatar saboda bullar cutar korona.

United wadda ke buga gasar Europa League ta bana tana mataki na biyar a kan teburin Premier League shekarar nan.

Cikin watan Yuni ake sa ran ci gaba da gasar Premier ta 2019-20, bayan da Liverpool ke mataki na daya a kan teburi da tazarar maki 25 tsakaninta da Manchester City ta biyu.

Ranar Talata kungiyoyin da ke buga Premier suka fara atisaye a mataki na cikin rukuni kamar yadda gwamati ta tsara don gudun yada cutar korona.