Manchester United ta ja kunnen magoya bayanta

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta bukaci magoya bayanta da su yi nisa da filin Old Traford da zarar an koma ci gaba da gasar Premier ta bana.
Mahukuntan gasar na ta tsare-tsaren yadda za a ci gaba da wasannin da suka rage na bana tun daga ranar 12 ga watan Yuni.
Sai dai kuma za a ci gaba da wasannin ne ba tare da 'yan kallo ba, hakan ne ya sa United ta fara biyan kudin tikikin kallon wasanni da suka rage mata a gida.
Ranar Laraba ne kungiyar ta Old Trafford za ta fara atisaye amma na yan wasa kadan a cikin rukuni kamar yadda aka tsara hanyoyin hana yada cutar korona.
Wasa hudu ne United za ta buga a gida hakan ya sa kungiyar ta bukaci magoya baya da su yi zamansu a gida, za kuma ta biya wadanda suka sayi tikin karawar da suka rage mata a gidan.
Haka kuma kungiyar na fatan magoya bayanta ba za su yi kokarin binta wasannin da za ta buga a waje ba, domin suma ba 'yan kallo za a yi su.
Cikin watan Maris aka dakatar da wasannin Premier tun bayan da cutar korana ta bulla, kuma Liverpool ce ta daya a kan teburi.
Manchester United wadda ke buga gasar Europa League tana ta biyar a kan teburi da maki 45, bayan da ta buga wasa 29.











