Marcus Rojo zai tattauna da Man United bayan karya dokar hana fita

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United za ta tuhumi Marcos Rojo, bayan da ya karya dokar da Argentina ta kafa ta hana zirga-zirga don gudun yada cutar korona.
An saka hotunan Rojo a kafar sada zumunta tare da abokanansa suna zukar taba da wasan kwallon teburi.
Dan uwan Rojo wato Franco ne ya saka hotunan a kafarsa ta sada zumunta daga baya ya goge su.
Kawo yanzu Rojo yana buga wasannin aro a kungiyar Estudiantes.
Argentina ta kafa dokar hana fita da za ta cika ranar 10 ga watan Mayu.
Rojo mai shekara 30, shi ne dan kwallon Premier na baya bayannan da ya karya dokar hana fita.
Ana zargi dan kwallon Aston Villa, Jack Grealish da Kyle Walker na Manchester City da dan wasan Everton, Moise Kean da karya dokar da gwamnati ta kafa tun bayan da aka rufe wasannin Premier a cikin watan Maris.







