Celtic aka bai wa kofin Scotland Hearts ta fadi daga wasannin bana

Asalin hoton, SNS
An bai wa Celtic kofin gasar kwallon kafar Scotland kuma karo na tara a jere, yayin da Hearts ta fadi daga wasannin bana, bayan da aka hakura da karawar da suka rage.
An cimma wannan matsaya ne, bayan wani taro da aka yi ranar Litinin, inda kungiyoyi 12 da ke buga gasar a makon jiya suka amince ba za a iya kammala sauran karawar da suka rage ba ta 2019-20.
An yi amfani da matsakaicin maki da kungiya ta samu a kowanne wasa wajen zakulo Zakara da wadanda suka fadi daga wasannin shekarar nan.
Sauyin da aka samu daya ne kafin a tsayar da gasar ranar 13 ga watan Maris, shi ne St Johnson da ta koma mataki na shida ita kuwa Hibernian ta koma ta bakawi a teburi.
Celtic ce ta daya a kan teburi da tazarar maki 13 tsakaninta da Rangers ta biyu, bayan buga wasa 30 da ya rage saura fafatawa takwas a karkare kakar bana.
An dakatar da dukkan wasannin tamaula a Scotand zuwa 10 ga watan Yuni, yayin da UEFA ta bukaci mambobinta su sanar da ita ko za su iya kammala kakar bana.
Ana sa ran fara kakar 2020=21 a gasar kwallon kafa ta Scotland ranar 1 ga watan Agusta.








