Kungiyar Celtic za ta rage albashin 'yan wasanta

Neil Lennon

Asalin hoton, Getty Images

Kocin Celtic, Neil Lennon ya ce watakila su rage albashin 'yan wasa, sakamakon tabarbarewar tattalin arziki saboda coronavirus.

Kungiyar Hearts ce ta farko mai buga gasar kwallon kafar kasar Scotland da ta bukaci 'yan wasanta su amince su zabtare albashinsu zuwa kaso 50 cikin 100.

Sauran wasa takwas ya rage a kammala gasar Premier ta Scotland ta kakar bana, kuma Celtic ce ke kan gaba a teburi da tazarar maki 13.

Kuma kungiyar na harin lashe kofi na tara a jere na gasar Premier Scotland.

Celtic ta sanar da samun ribar fam miliyan 24 na wata shidan karshe na shekarar bara, wadda ta karkare shekarar 2019 da ribar da ta kusan kai fam miliyan 33.