Mutum 300 aka amince a lokacin buga Bundesliga a fili

Za a ci gaba da gasar Bundesliga ranar Asabar karawar mako na 26 ba tare da 'yan kallo ba, bayan da aka dakatar da wasanni saboda bullar cutar korona.

Yayin da ake shirin ci gaba da wasannin ba 'yan kallo, an kuma tanadi tsare-tsare da matakai da kungiyoyin za su bi a lokacin gasa.

Mutum 300 aka amince su shiga filin wasa don gudanar da gasa a makon, an kuma raba su zuwa rukuni uku da ke da mutun 100 kowanne.

Rukunin farko ya hada da cikin filin da za a taka leda da wurin sauya kayan 'yan kwallo, kuma wadanda aka amince wa a wurin sun hada da 'yan wasa da masu zaman benci da masu horar wa da alkalin wasa da yara masu dauko kwallo da jami'an lafiya da jami'an tsaro da na tsabtar muhalli da kada su wuce mutum 100.

Rukuni na biyu zai kunshi wurin zama ba 'yan kallo sai dai 'yan jarida da masu kamara da wadanda ke aikin kula da allo da sauran na'urori kar su wuce mutun 100.

Rukuni na uku ya kunshi wajen fili daga baya kenan, inda jami'an tsaro za su tsaya don hana mutune zuwa kusa da ginin filin.

Kowace kungiya za ta nada jami'in tsabtar muhalli wanda zai dinga bayar da shawarwari.

Yara masu dauko kwallo hudu aka amince su shiga fili kuma masu shekara 16, za kuma su dunga fesa magani a hannunsu, sannan za a dinga yi wa kwallon feshin magani kafin wasa da kuma a lokacin da ake fafatawa.

Ba a amince butum-butumin kungiya ya shiga fili ba har da kananan yara, sannan babu gaisawa hannu da hannu kuma babu yin hoton kungiya.

Za kuma a rufe dakin da 'yan jarida ke hira da 'yan wasa da masu horas da su, sai dai a yi ta bidiyon zamani.

Kowanne dan wasa sai ya saka takunkumi ban da wadanda ke taka leda, amma mai horar wa da masu zaman benci sai sun saka, sannan su bayar da tazarar wajen zama.

Ba za a amince da masu dafa abinci ba, saboda haka kowace kungiya ta tanadi abin da za ta ci a kuma kai fili tun kafin a bukata.