Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Union Berlin za ta koma buga gasar Bundesliga ba koci
Ranar Asabar 16 ga watan Mayu za a ci gaba da gasar Bundesliga karawar mako na 26 ba tare da 'yan kallo ba.
Sai dai kuma Union Berlin za ta ci gaba da kakar bana ta 2019-20 ba tare da mai horas da ita ba, bayan da Urs Fischer ya bar sansanin horon kungiyar ranar Laraba.
Kocin dan kasar Switzerland ya bar otal din da yake zaune Lower Saxony don radin kansa, kamar yadda Union Berlin ta sanar ta kuma ce mataimakinsa ne zai ja ragamar kungiyar.
Bundesliga za ta zama gasa ta farko da za a ci gaba da wasanni a Turai tun bayan da cutar korona ta haddasa tsaiko cikin watan Maris.
Union ta ce kocin ya bar kungiyar ne don radin kansa, kuma babu batun ko ya kamu da cutar korona ko karya dokar gwamnati ta killace kai, kafin a ci gaba da Bundesliga.
Tuni kungiyar ta bai wa mataimakin koci Markus Hoffmann da kuma Sebastian Boenig aikin horas da 'yan wasa don karkare wasannin da suka rage mata.
Union Berlin wadda ta hau gasar Bundesligar bana tana mataki na 11 a kan teburi da tazarar mako 30 tsakaninta da kungiyoyin da ke karshen teburi, hakan na nufin za ta ci gaba da buga gasar badi kenan.