Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ranar Asabar za a ci gaba da gasar Bundesliga ta Jamus
Ranar Asabar za a ci gaba da gasar cin kofin Bundesliga ta bana, bayan da gwamnatin Jamus ta amince a karkare kakar 2019-20 ba tare da 'yan kallo ba.
Bayan da aka buga wasannin mako na 25 ne aka dakatar da dukkan wasannin Bundesliga cikin watan Maris, saboda tsoron hana yada cutar korona.
Tun bayan da annobar ta yadu ne gwamnatin Jamus ta kafa dokar hana fita da zirga-zirga da kuma bayar da tazara idan za a fita waje.
Bayern Munich ce ta daya a kan teburi da maki 55, sai Borrusia Dortmund da maki 51, sannan RB Leipzig ta uku da maki uku.
Wadanda suke kasan teburi sun hada da Fortuna Dusseldorf da maki 22 a mataki na 16, sai Werder Bremen ta 17 da maki 18, sannan Paderborn ta 18 da maki 16.
Dan wasan Bayern Munich, Robert Lewandowski shi ne kan gaba da kwallo 25 a raga, sai Timo Werner na RB Leipzig mai 21 da kuma Jadon Sancho na uku da kwallo 14 a raga.
Bayern Muinch mai rike da kofi ta lashe sau bakwai a jere tana da Bundesliga 29 jumulla.
A cikin watan Agusta ake sa ran karkare gasar Zakarun Turai ta Champions League a Instanbul.
Jadawalin wasannin mako na 26 da za a ci gaba da yi:
Wasannin ranar Asabar 16 ga watan Mayu
- BV Borussia Dortmund da Schalke 04
- TSG 1899 Hoffenheim da Hertha Berlin
- FC Augsburg da Wolfsburg
- Fortuna Dusseldorf da Paderborn 07
- RB Leipzig da Freiburg
- Eintracht Frankfurt da Borussia Monchengladbach
Wasannin ranar Lahadi 17 ga watan Mayu
- FC Koln da FSV Mainz 05
- FC Union Berlin da Bayern Munich
Wasan da za a yi ranar Litinin 18 ga watan Mayu
- SV Werder Bremen da Bayer 04 Leverkusen