Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bundesliga: Dynamo Dresden ta killace dukkan 'yan wasanta
Dynamo Dresden wadda ke buga karamar gasar Bundesliga ta killace dukkan 'yan wasanta da masu horas da ita, mako biyu kan a ci gaba da wasannin 2019-20.
Kungiyar ta yi hakan ne, bayan da ta samu 'yan wasa biyu dauke da cutar korona.
Ranar Asabar 16 ga watan Maris za a ci gaba da wasannin Bundesliga da mai biye da ita don karkare kakar bana,
Gasar ta Jamus ita ce ta farko da za a ci gaba da ita a nahiyar Turai tun bayan bullar cutar korona da ta tsayar da komai.
Kimanin jami'ai da 'yan wasa da ma'aikata 300 ake sa ran su kasance cikin fili a lokacin da ake gudanar da wasannin ba tare da 'yan kallo ba.
An tsayar da wasannin Bundesliga ranar 13 ga watan Maris, sai dai cikin watan Afirilu 'yan wasa suka fara atisaye bisa matakan kariya na hana yada annobar.
Dresden ita ce ta karshe a kasan teburi a karamar gasar Bundesliga. ,