Everton za ta hukunta Moise Kean, bayan da ya karya dokar hana fita

Moise Kean

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Moise Kean ya koma Everton daga Juventus kan fam miliyan £25.1 a kakar bana

Kungiyar Everton za ta hukuntan Moise Kean, bayan da hotunan dan wasan suka bayyana ya hada taron shagali a gidansa.

Hakan kuma ya karya dokar da Gwamnatin Burtaniya ta saka na kaucewa yada cutar korona.

Watakila Everton ta ci tarar dan kwallon, bayan da ta ce ta ji takaici, bayan wasu hotuna da aka nuna dan kwallonta Moise Kean.

Daily Star ta ranar Lahadi ta ruwaito cewar dan kwallon tawagar Italiya mai shekara 20 ne da kansa ya dauki hotunan shagalin da aka gudanar a gidansa.

Everton ta ce "Ta ji takaici da dan wasanta ya karya dokar gwamnati da wadda kungiyar ta gindaya don kaucewa yada cutar korona."

Kungiyar ta kara da cewar "Ba ta ji dadin abin da dan kwallon ya yi ba."

Everton ta kara da cewar "tana fadakar da dukkan 'yan kwallonta muhimmancin bin dokar da gwamnati ta kafa - har da shawarwari na abin da ya kamata mutum ya yi a gida da waje - Inda ta ke tuntubar 'yan wasa.

Daga ranar 27 ga watan Afiriru sama da mutum 20,000 cutar korona ta kashe a Burtaniya a asibiti kamar yadda hukumar lafiya ta sanar.

Keane bai fara wasa da kafar dama a Everton ba tun bayan da ya koma kungiyar daga Juventus kan fam miliyan 25.1, inda ya ci kwallo daya tal a gasar Premier.

Dan kwallon ya koma zaman benci a wasa da Southampton a watan Nuwamba, bayan da koci Marco Silva ya hukunta shi, bayan da ya yi lattin zuwa taron kungiya kuma karo na biyu.

Keane shi ne na baya-bayan nan da ya karya dokar hana fita saboda hana yada cutar korona.

Kyale Walker na jiran hukuncin da Manchester City za ta yi masa, bayan da ya hada fati tare da wasu karuwai biyu.

'Yan wasan Tottenham Serge Aurier da Moussa Sissoko sun nemi gafara, bayan da suka yi atisaye a tare ba tare da bayar da tazara ba.

Shi kuwa Jose Mourinho ya amsa cewar ya karya doka bayan da yake bai wa Tanguy Ndombele atisaye ba tare da tazara ba.