Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Premier League: Ancelotti ya zama kocin Everton
Kungiyar Everton ta nada Carlo Ancelotti a matsayin kocinta na dindindin a yarjejeniyar shekara hudu da rabi.
Dan kasar Italiyan wanda Napoli ta kora a farkon watan nan, ya maye gurbin Marco Silva ne da Everton din ta kora ranar 6 ga watan Disamba.
Ancelotti wanda ya lashe kofin Zakarun Turai ta Champions League sau uku, ya dawo Ingila da aiki shekara takwas da rabi bayan Chelsea ta kore shi.
"Karara take cewa mai kulob din yana son kawo nasarori," in ji shi.
Duncan Ferguson ne ya ci gaba da jan ragamar kulob din na rikon kwarya, kuma zai ci gaba da zama a matsayin daya daga cikin mataimakan Ancelotti.
Sabon kocin ya halarci wasan da Everton ta yi canjaras da Arsenal a yau Asabar kuma zai karbi aikin a hukumance ranar lahadi.