Barcelona vs Getafe: Barca ta ci wasan waje na farko

Luis Suarez

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Suarez ne da Firpo suka ci wa Barcelona

Barcelona ta ci wasan waje na farko a gasar La Liga ta bana tun watan Afrilu bayan ta casa Getafe ranar Asabar a filin wasa na Estadio Coliseum Alfonso Perez.

Luis Suarez ne ya fara ci kafin tafiya hutun rabin lokaci a wani abin da ba a saba gani ba, inda mai tsaron raga Ter Stegen ya taimaka masa.

Junior Firpo ne ya kara ta biyun bayan mai tsaron raga Soria ya amayar da kwallon da aka dada masa, inda shi kuma ya harba ta cikin raga jim kadan bayan hutun rabin lokaci.

Saura minti takwas a tashi daga wasa ne kuma aka kori Clement Lenglet na Barcelona bayan an ba shi katin gargadi na biyu.

Bayan rashin lafiya da Messi ke fama da ita, shi ma Ousmane Dembele yana benci bayan ya ji rauni.

Kazalika shi ma matashin dan wasa Ansu Fati ya ji raunin, abin da ya bai wa Carles Perez damar shiga gaban tawagar domin bugawa tare da Suarez da Antonie Griezmann.

Kamar yadda aka saba gani a wannan kakar idan Barcelona na wasa a waje, sukan rasa dabarun cin kwallo, amma wannan karon sai ga shi ta ci kwallon amma ba ta hanyar da aka saba gani ba.

Nasarar ta daga Barca zuwa mataki na biyu da maki daya tsakaninta da Real Madrid, wacce za ta fafata da abokiyar hamayyarta ta birnin Madrid wato Atletico da karfe 8:00 na daren yau Asabar.