NACA: An samu raguwar masu kamuwa da HIV a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar yaki da cuta mai karya garkuwar jiki a Najeriya wato NACA ta ce an samu matukar raguwa kan yadda cutar ke yaduwa a kasar.
Ta ce an samu raguwar ce da kimanin kashi 60 cikin 100 daga shekara ta 2005 zuwa bara.
A cewar hukumar NACA, har yanzu jihohin kudancin kasar ne ke kan gaba a yawan masu dauke kwayar cutar.
Dr Aliyu Gambo shi ne babban jami'in NACA a Najeriya, ya ce a shekara ta 2005 mutum 9 daga cikin kowane mutum 200 na dauke da kwayar cutar.
Sai dai a cewarsa a bara an gano cewa mutum 4 ne cikin 200 ke dauke da cutar.
Shugaban na NACA ya ce an samu nasarar rage yaduwar cutar ne saboda magungunan da masu HIV din ke sha, wadanda ke dakushe kaifinta.
Sai dai NACA din ta ce har yanzu akwai mutane masu dauke da HIV wadanda ba su je an gwada su ba balle su fara shan magani.
Haka nan kuma akwai wadanda sun san suna dauke da cutar amma ba su iya zuwa karbar magani saboda gudun tsangwama da kyama.
Wani mai dauke da cutar ta HIV a Kano ya tabbatar wa BBC cewa duk da a baya sun fuskanci kalubale na rashin maganin da suke sha, to amma a yanzu maganin ya wadata.











