Za a samar da riga-kafin HIV

Allurar riga-kafi

Asalin hoton, Getty Images

Masu bincike a bangaren lafiya sun ce an samu ci gaba a yunkurin da aka jima ana yi wajen neman riga-kafin ciwon HIV bayan da aka yi gwajin wani sabon magani a kasashe daban-daban.

Maganin ya na zaburar da garkuwar mutanen da ba sa dauke da cutar, kuma alamu sun nuna cewa ba shi da illa.

Wata tawaga wadda bangaren kiwon lafiya a jami'ar Havard ya jagoranta ne suka yi gwajin maganin riga-kafin a kan mutane kusan 400 da suka nuna sha'awar a yi gwajin da su a kasashen Gabashin Afirka da Kudancin Afirka da Thailand da kuma Amurka.

Masana kimiyya dai sun bayyana sakamakon da cewa abu ne mai matukar muhimmanci da aka cimma, sai dai kuma sun bukaci cewa ayi taka tsan-tsan.

Nan gaba kadan za a sake wani gwajin maganin riga-kafin a kan mata fiye da 2000 a Kudancin Afirka.

Karanta wasu karin labaran