Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal ta sayi Gabriel Martinelli
Arsenal ta kammala sayen dan Brazil Gabriel Martinelli, mai shekara 18 da haihuwa.
Dan kwallon ya sanya hannu a yarjejeniyar kasancewa da kungiyar "ta tsawon lokaci" kamar yadda kungiyar ta bayyana.
Martinelli ya koma Arsenal ne daga kungiyar Ituano da ke Brazil, inda ya ci mata kwallo 10 a wasanni 34 bayan fara taka mata leda a shekarar 2017.
"Ina koyi da salon wasan Cristiano Ronaldo ne," in ji Martinelli.
"Wannan dan wasa ne mai aiki tukuru inda yake samun ci gaba. A koyaushe yana kokarin cinye kofuna da lambobin yabo."
Ya ci gaba da cewa: "Wannan ne burin da nake da shi tun lokacin da nake karami kuma mutanen gida sun yi fatan buga wasa a nahiyar Turai a babbar kungiya kamar Arsenal. Na karbi wannan dama hannu biyu-biyu."
Martinelli yana cikin 'yan wasan da aka kira don su taka leda a tawagar wasan Brazil a lokacin da suke wasannin tunkarar Gasar Copa America.
"Na ji dadi sosai tun da mafarkina ya zama gaske, zan kasance kusa da manyan 'yan wasa." in ji shi.
"Wannan babbar dama ce ta koyo da kuma jin dadi yadda ya kamata."