Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
AFCON: Yi hasashen kasar da za ta yi nasara a gasar kofin Afirka
An fara wallafa wannan makala ranar 8 ga watan Yulin 2019.
Za a gudanar da gasar cin kofin nahiyar Afirka da Masar za ta karbi bakunci ta 32 daga ranar 21 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yulin 2019.
A karon farko hukumar kwallon kafar Afirka, CAF, ta amince a 2017 da sauya lokacin da ake yin wasannin daga Janairu zuwa Fabrairu, inda ya koma tsakanin Yuni zuwa Yuli, kuma aka kara yawan kasashen da za su fafata daga 16 zuwa 24.
Tun farko an tsara cewar Kamaru ce za ta karbi bakuncin gasar ta 2019, kuma karo na farko tun 1972, daga baya aka karbe izinin gudanar da wasannin sakamakon rashin ingantaccen shiri da batun Boko Haram da sauran matsaloli.
Tun farko CAF ta tsara cewar za a fara gasar ta bana tsakanin 15 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yuli, amma sakamakon Azumin watan Ramadan ya sa hukumar ta maida lokacin daga 21 ga Yuni zuwa 21 ga watan Yuli.
Ku shiga wannan adireshin na kasa don yin hasashen yadda wasannin za su rinka gudana: