Arsenal ta taya Zaha fan miliyan 40

    • Marubuci, Daga David Ornstein
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport

Arsenal ta mika tayin farko na fan miliyan 40 domin sayen dan wasan Crystal Palace Wilfried Zaha.

Babu wani dan wasa da aka hada da shi a tayin, wanda ake sa ran Palace za ta yi watsi da shi.

Dan wasan mai shekara 26 na so ya bar kulob din kuma ya fi so ya koma Arsenal, amma Palace ta yi wa dan kwallon na Ivory Coast farashin fan miliyan 80.

Arsenal za ta so gannin an sassauta farashin sannan a amince mata ta biya kudin da kadan-kadan.

Yukurin Arsenal na sayen 'yan wasa a wannan kaka ya fuskanci nakasu saboda kasa zuwa gasar Zakarun Turai ta badi da ta yi.

Dan uwan Zaha, Judicael, ya shaida wa told Sky Sports News cewa: "Ganin irin rawar da Wilfried ya taka a Crystal Palace, ina fatan Palace za su duba hakan domin cimma yarjejeniya da Arsenal da za ta ba shi damar buga gasar Turai a kulob din da ya dade yana marawa baya tun yana karami."