Ahmed Musa ya koma Saudiyya murza leda

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Najeriya Ahmed Musa ya koma kungiyar Al-Nassr ta kasar Saudiyya, kamar yadda kungiyar Leicester City ta bayyana.
Sai dai kungiyar Leicester ba ta bayyana kudin da ta sayar da dan kwallon ba.
Dan wasan mai shekara 25 ya koma Leicester City ne daga CSKA Moscow a shekarar 2016.
Bayan ya zura kungiyar kwallaye biyu kacal a wasanni 21, sai aka mayar da shi tsohuwar kungiyarsa aro a kakar bara.
Dan wasan ya taka wa Najeriya leda a gasar cin kofin duniya a Rasha, inda ya ci wa kasar kwallaye biyu a wasan da kasar ta doke Iceland da ci 2-0.
Sabuwar kungiyarsa ta yi masa maraba a shafinta na Twitter, inda ta wallafa wani bidiyo da yake nuna yadda dan wasan ya zura wasu kwallaye a raga.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X






