Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sergio Aguero ya karya kashin hakarkari
Dan wasan gaban Manchester City, Sergio Aguero, ya karya kashin hakarkarinsa a wani hatsarin mota da ya yi a birnin Amsterdam na kasar Holland a daren ranar Alhamis.
Yayin da kocin kungiyar Pep Guardiola ya ce tabbatar da hakan, ya ce ba shi da matsala game da jinyar da dan wasan zai yi.
An ba da rahoton cewar dan kasar Argentina mai shekara 29 yana hanyar shi ta zuwa filin jirgin sama ne a motar haya bayan ya kalli wakar da mawaki Maluma ya yi.
City ta ce "ya kasance a kasar Holland ne a lokacin hutunsa, kuma ya ji raunuka".
Ana tsammanin Aguero ya koma Manchester ranar Juma'a, kuma likitocin City za su gwada shi kafin tafiyarsu wasan gasar Firimiya a Chelsea ranar Asabar.
'Yan sanda a Amsterdam sun tabbatar wa BBC cewar mutum biyu ne cikin motar tasi din da ta yi hatsari a unguwar De Boelelaan da ke cikin birnin.
Kafin hatsarin dai, dan kwallon ya wallafa hotonsa da mawaki Maluma a shafinsa na Instagram da sakon da ke cewa: "ina godiya da gayyatata".
Tsohon kulob din Aguero, Independiente, ya tura wa dan wasan sakon fatan alkhairi ta shafin Twitter, yana mai cewa"Kuzari tare da warkewa cikin gaggawa ga aguerosergiokun! Ilahirin @Independiente na tare da kai a wannan mawuyacin lokaci."
Dan wasan gaban ya ci kwallaye bakwai a wasanni takwas a Man City a wannan kakar.
Kuma ya tallafa wa kungiyar Pep Guardiola ta hau saman teburin gasar Firimiya tare da yin nasara a wasanninsu biyu na farko a gasar zakarun Turai.