Europa: Arsenal ta yi rawar-gani, ta doke Bate 4-2

Theo Walcott ya zura kwallo biyu a raga a wasan da Arsenal wadda bisa ga dukkan alamu ta farfado daga yanayin da ta shiga na rashin katabus, inda ta doke Bate Boristov a wasan Europa.

Wasan da suka tashi 4-2, ranar Laraba, ya kasance na biyu da Arsenal ta ci a rukuninsu na takwas (Group H) na gasar kofin Turai ta Europa.

Walcott ya fara daga raga ne a minti na tara da shiga fili, sannan ya kara ta biyu a minti na 22.

Rob Holding ya ci wa Arsenal kwallonsa ta farko a minti na 25, wadda ta kasance ta uku ga kungiyar, kafin kuma Giroud shi ma ya ci tasa a minti na 49 da bugun fanareti, kwallon da ta kasance ta 100 da ya ci wa kungiyar.

Bate ta samu kwallayenta ne ta hannun Ivanic a minti na 28 da shiga ili, yayin da a minti na 67 Gordeychuk ya ci musu ta biyu.

Arsenal ce kungiya ta farko da ta doke Bate a gida a wata gasar kofin Turai, tun bayan da Barcelona ta ci ta a wasan rukuni na kofin zakarun Turai a 2015- a wasa bkawai kenan.

Arsenal ce ta daya yanzu a rukunin da maki shida, yayin da Red Star Belgrade take zaman ta biyu da maki hudu, bayan da ta ci Cologne, wadda ta sha kashi a wasanninta biyu, da daya mai ban haushi.

A karawar da aka yi tsakanin Everton da Apollon Limassol, Sardinero Corpa ne ya fara daga ragar Everton a minti na 12, kafin Rooney ya rama a minti na 21.

Vlasic ya ci wa mai masaukin baki Everton ta biyu a minti na 66, kafin kuma can a minti na 88 Yuste Canton ya rama wa bakin.

Everton ta ci gaba da kasancewa ta karshe a rukuninsu na biyar (Group E), bayan da Lyon ta yi kunnen-doki 1-1 da Atalanta.

Ga sakamakon sauran wasannin na Europa na ranar Alhamis :

Östersunds FK 1-0 Hertha BSC

Everton 2-2 Apollon Limassol

FC Astana 1-1Slavia Prague

Ath Bilbao 0-1 Zorya Luhansk

Lazio 2-0 SV Zulte Waregem

Nice 3-0 Vitesse

Rosenborg 3-1 Vardar

Zenit St P 3-1 Real Sociedad

Lugano 1-2 Steaua Buc

Viktoria Plzen 3-1Hapoel Be'er Sheva

FC Köln 0-1Crvena Zvezda

FC Red Bull Salzburg1-0 Marseille

Konyaspor 2-1Vitória Guimarães

Sheriff Tiraspol 0-0 FC Copenhagen

Lokomotiv Moscow 3-0 Zlín

Lyon 1-1 Atalanta

Ludogorets Razgrad 2-1 Hoffenheim

AC Milan 3-2 HNK Rijeka

AEK Athens 2-2 Austria Vienna

Sporting Braga 2-1 Istanbul Basaksehir

Skenderbeu 1-1 Young Boys

Partizan Belgrade 2-3 Dynamo Kiev

Zenit St Petersburg 3-1 Real Sociedad

Rosenborg 3-1 Vardar