Sergio Aguero ya karya kashin hakarkari

Manchester City's Sergio Aguero

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Sergio Aguero ya buga wasan da Manchester City ta doke Shakhtar Donetsk 2-0 ranar Talata

Dan wasan gaban Manchester City, Sergio Aguero, ya karya kashin hakarkarinsa a wani hatsarin mota da ya yi a birnin Amsterdam na kasar Holland a daren ranar Alhamis.

Yayin da kocin kungiyar Pep Guardiola ya ce tabbatar da hakan, ya ce ba shi da matsala game da jinyar da dan wasan zai yi.

An ba da rahoton cewar dan kasar Argentina mai shekara 29 yana hanyar shi ta zuwa filin jirgin sama ne a motar haya bayan ya kalli wakar da mawaki Maluma ya yi.

City ta ce "ya kasance a kasar Holland ne a lokacin hutunsa, kuma ya ji raunuka".

Ana tsammanin Aguero ya koma Manchester ranar Juma'a, kuma likitocin City za su gwada shi kafin tafiyarsu wasan gasar Firimiya a Chelsea ranar Asabar.

'Yan sanda a Amsterdam sun tabbatar wa BBC cewar mutum biyu ne cikin motar tasi din da ta yi hatsari a unguwar De Boelelaan da ke cikin birnin.

Kafin hatsarin dai, dan kwallon ya wallafa hotonsa da mawaki Maluma a shafinsa na Instagram da sakon da ke cewa: "ina godiya da gayyatata".

Sergio Aguero accident in Amsterdam

Asalin hoton, KaWijKo Media

Bayanan hoto, Hatsarin ya auku ne a unguwar De Boelelaan na Amsterdam

Tsohon kulob din Aguero, Independiente, ya tura wa dan wasan sakon fatan alkhairi ta shafin Twitter, yana mai cewa"Kuzari tare da warkewa cikin gaggawa ga aguerosergiokun! Ilahirin @Independiente na tare da kai a wannan mawuyacin lokaci."

Dan wasan gaban ya ci kwallaye bakwai a wasanni takwas a Man City a wannan kakar.

Kuma ya tallafa wa kungiyar Pep Guardiola ta hau saman teburin gasar Firimiya tare da yin nasara a wasanninsu biyu na farko a gasar zakarun Turai.

Sergio Aguero and Maluma

Asalin hoton, 10aguerosergiokun

Bayanan hoto, Sergio Aguero (daga hagu ) da Maluma a wani hoton da ya wallafa a shafin Instagram sa'o'i kafin hatsarin motar