Kofin FA: Hull City ta kafa tarihi

Hull City za ta kara da Arsenal a wasan karshe ranar 17 ga watan Mayu a Wembley.

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto, Hull City za ta kara da Arsenal a wasan karshe ranar 17 ga watan Mayu a Wembley.

Hull City ta kai wasan karshe a karon farko tun da aka kafata bayan ta buge Sheffield United da ci 5-3.

Da wannan nasara Hull City za ta kara da Arsenal a wasan karshe na kofin na FA ranar 17 ga watan Mayu a Wembley.

Sheffield sun fafata da Hull City din ba tare da wata fargaba ba ta cewa Hull City na gasar Premier ganin yadda 'yan wasan suka dage.

Rashin nasarar ya hana kociyan Sheffield Clough kafa tarihin da mahaifinsa Brian ya yi, wanda ya kai Nottingham Forest wasan karshe na FA, inda Tottenham ta buge ta.