Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: 'Yan Najeriya na kukan rashin abinci
Al'ummar Najeriya na ci gaba da korafi kan yanayin da kasar ta fada na rashin wadatar abinci yayin da mahukunta ke sake tsaurara matakan dakile cutar korona.
A 'yan kwanakin nan ana samu karuwar korafin yunwa a sassa daban-daban na kasar musamman a arewaci inda galibin al'ummarta ke rayuwa irinta hannu baka hannu kwarya.
Gwamnatoci jihohi da na tarayya sun ce suna daukar matakan ragewa marassa karfi radadin talauci ta hanyar rabon tallafin abinci da kudi yayin da suke ci gaba da daukar matakan shawo kan annobar.
Sai dai da alama wannan tallafi bai wadatar ba, ganin yadda ake samun karuwar masu korafi da kukan yanayin yunwa a yankuna da dama na kasar.
Wannan hali da kasar ke ciki ya sa kungiyoyi da dai-daikun mutane ankarar da shugabanni da masu hannu da shuni domin kai wa mutane marassa karfi taimako.
Daya daga cikin irin kungiyoyin da ke wannan kira akwai ta matasan arewa maso gabashin Najeriya.
Shugaban kungiyar Alhaji Abdurahaman Buba Kwacham, ya shaida wa BBC cewa suna da shakku kan fitar da tallafin da ake cewa ana rabawa al'umma a fadin kasar.
Ya ce ''Babu shakka yanayin da ake ciki jarrabtace ta Ubangiji amma a gaskiya ana rabewa da guzuma ana harbin karsana''.
''Akwai dodorido kan batun wannan tallafin babu adalci, misali jihar Adamawa da Kebbi tireloli uku uku aka kai na shinkafa amma a Abuja an ce mana an raba tirela hamsin.''
Alhaji Abdurahman dai na ganin akwai cutarwa saboda an tursasawa al'umma bin doka da oda amma ana musguna musu da yunwa.
'Kalubale'
Tun bayan lokacin da gwamnati ta sanya dokar takaita zirga-zirga a wasu manyan biranen kasar ake ta guna-guni a kan yadda hakan ke shafar tattalin arzikin dai-daikun mutane.
Yayin da kasar ke sake samun karuwar alkaluman masu dauke da wannan cuta da yanzu haka suka zarce dubu, ana diga ayar tambaya kan makomar al'ummarta idan aka ci gaba da zaman killace kai.
Fauziyya D. Sulaiman jagora ce ta irin kungiyoyin da ke tallafawa al'umma musamman a wannan lokaci da Azumin Ramadana ya riske musulmi cikin annoba.
Ta shaida wa BBC cewa suma ayyukansu na fuskantar cikas ganin cewa a baya a sawwake suke rabon kayan abinci amma yanzu abin na basu wahala saboda yanayin da kasar ke ciki.
Fauziyya ta ce babban kalubalensu shi ne isa wurin mabukata domin tallafa musu a wannan yanayi na annoba da rayuwar killace kai.
'Tattalin arziki'
Zuwa yanzu dai cutar korona ta yadu a jihohi 27 na Najeriya hadi da Abuja. Kuma da alama sassauta dokar hana zirga-zirga da aka kafa a galibin jihohin kasar zai dau lokaci kafin a sassauta.
A ranar Litinin wa'adin dokar hana fita ta tsawon mako biyu da shugaba Buhari ya tsawaita a jihohin Legas da Ogun da kuma babban birnin Tarayya Abuja domin dakile yaduwar cutar korona za ta kawo karshe.
A kallum kuma cutar korona kara yawa take inda ake samun karuwar masu dauke da cutar, da kuma yadda take kara yaduwa a sassan Najeriya.
Ba Najeriya kawai ba ce kasar da tattalin arzikinta ko na al'ummarta wannan yanayi na annoba ya shafa ba, akwai kasashen duniya da dama da suma ke fama da matsaloli tattalin arziki sakamakon annobar.
Bankin duniya ya yi hasashen cewa duniya za ta dau tsawon lokaci kafin ta farfado daga tasirin da wannan annoba.