Yadda China ke shirin zama gagarumar ƴar sama jannati fiye da kowa

Chinese flag in space with the Earth in the background

Asalin hoton, BBC; Getty Image; Nasa

    • Marubuci, Daga Wanyuan Song and Jana Tauschinski
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

Ƴan sama jannatin China uku sun fara wani aiki na wata shida don kafa sabuwar tashar sararin samaniyar ƙasarsu.

Wannan shi ne shiri na baya-bayan nan da China ke yi a ƙoƙarinta na fin sauran ƙasashen samun iko da zama jagora a nazarin sararin samaniya nan da gomman shekaru masu zuwa.

Mece ce tashar sararin samaniya ta Tiangong?

A bara, China ta aika da kumbo na farko na tashar Tiangong zuwa sararin samaniya. Tana da shirin ƙara wasu kumbon zuwa ƙarshen shekara.

Zuwa shekara mai zuwa, za ta ƙaddamar da wani kumbon zuwa sararin samaniya mai suna Xuntian.

Wannan kumbon zai tashi ya sauka a kusa da Tiangong domin yi masa gyara da kuma ƙarin mai.

Tiangong za ta samar wa kanta wuta da sauran abubuwa da wuraren zama.

China ita ce ƙasa ta uku a tarihin duniya da ta aika da ƴan sama jannati sararin samaniya ta kuma gina tashar sararin samaniya, bayan ƙungiyar Tarayyar Soviet da kuma Amurka.

1px transparent line

China na da burin da take so cimmawa da Tiangong kuma ana sa ran za ta maye gurbin tashar sararin samaniya ta ƙasa da ƙasa wato ISS wadda za a rufe ta a 2031.

An cire ƴan sama jannatin ƙasar China daga ISS sakamakon dokar Amurka da ta haramta hukumar da ke kula da sararin samaniyarta wato Nasa bai wa China bayanai.

Shirin China na zuwa duniyar wata da Mars

Burin da China ke da shi bai tsaya a nan ba.

Shekaru kaɗan daga yanzu ana sa ran za ta ɗauki samfurin duwatsu na asteriod a kusa da duniyar Earth.

Zuwa shekarar 2030, tana da burin kai ƴan sama jannatinta zuwa duniyar wata, haka kuma za ta tura a samo samfarin abubuwa daga Mars da Jupiter.

1px transparent line

Me sauran ƙasashe suke yi?

A daidai lokacin da China ke ƙara faɗaɗa ayyukanta a sararin samaniya, wasu ƙasashen na ta ƙoƙarin tafiya duniyar wata.

Nasa na ƙoƙarin komawa duniyar wata tare da ƴan sama jannati daga Amurka da sauran ƙasashen duniya daga 2025 zuwa sama, haka kuma tuni ta fitar da sabon babban kumbonta a Kennedy Space center.

Japan Koriya Ta Kudu da Rasha da Indiya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa na ta ƙoƙarinsu na zuwa sararin samaniya,

Indiya ta ƙaddamar da shirinta na biyu mafi girma na zuwa duniyar wata haka kuma tana da niyyar samun tasharta zuwa shekarar 2030.

line

Wa yake tsara dokoki a sararin samaniyar?

  • Yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya ta 1967 ta ce babu wata ƙsa da za ta yi ikirarin iko da wani sashe a sararin samaniya
  • Yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya ta Moon Agreement ta 1979 ta ce bai kamata a mayar da sararin samaniya wani ɓigire na kasuwanci ba, amma Amurka da China da Rasha sun ƙi sanya hannu
  • A yanzu, Amurka na tallata manufofinta na yarjejeniyar ƙasa da ƙasa na zuwa sararin samaniya wato Artemis Accords
  • Rasha da China ba za su sanya hannu kan maufofin na Artemis Accords ba, suna masu cewa Amurka ba ta da damar tsara dokoki a sararin samaniya.
line

Mene ne tarihin China a sarrain samaniya?

China ta fara saka tauraron ɗan adam ɗinta na farko mai zagaye a sararin samnaiya a 1970 - a yayin da ta samu wani babban sauyi sakamakon gagarumin sauyin zamani da ta fuskanta.

Manyan ƙasashen duniyar da suka iya zuwa sarrain samaniya su ne Amurka da Rasha da Faransa da kuma Japan.

A cikin shekara 10 da suka gabata, China ta aika fiye da roka 200.

Kuma tuni ta aika wani jirgin sama jannati da ba a ba shi suna ba zuwa duniyar wata, a wani shiri na Chang'e 5, don tattaro samfurin duwatsu.

Ta kafa tutar ƙasar a duniyar wata - wacce ta fi ta Amurka da ke can girma.

A yanzu haka China tana da ƴan sama jannati 13 a sararin samaniya, idan aka kwatanta da 340 na Amurka da kuma fiye da 130 ɗin Rasha.

Sai dai an samu ƴan matsaloli. A shekarar 2021 wani ɓangare na rokar da China ta aika ya faɗo daga sararin samaniyar inda ya faɗa cikin Tekun Atalantika, sannan an sake samun matsalar ƙaddamar da wasu rokokin biyu a 2020.

1px transparent line

Wa yake ɗaukar nauyin shirin zuwan China sararin samaniya?

Kafar yada labarai ta China Xinhua ta ce akalla mutum 300,000 ne suka yi aiki a kan shirin kasar na sararin samaniya - wato kusan ninki 18 kan yadda Nasa ke aiki a kan sararin samaniya.

An kafa hukumar sararin samaniya ta China a 2003 inda da farko aka ware mata yuan biliyan biyu kwatankwacin ($300m, £240m) a matsayin kasafin kudinta.

Sai dai a shekarar 2016 China ta bai wa kamfanoni masu zaman kansu damar zuwa tasharta ta sararin samaniya, kuma yanzu haka an kashe fiye da yuan biliyan 10, kwatankwacin ($1.5bn, £1.2bn) a shekara daya, a cewar kafofin watsa labaran China.

1px transparent line

Me ya sa China za ta tafi sararin samaniya?

China tana matukar mayar da hankali a kan fasahar tauraron dan adam, domin bunkasa harkokin sadarwa, da hanyoyin sufirin juragen sama, da hasashen yanayi da makamantana su.

Amma da dama daga shirinta na bunkasa tauraron dan adam yana da alaka da harkokin soja. Yana taimaka mata wurin leken asirin 'yan hamayya, da makamai masu linzami da ke cin dogon zango.

Lucinda King, kwararriya kan sararin samaniya a Jami'ar Portsmouth, ta ce China ba tana mayar da hankali ne kan manya-manyan bincike na sararin samaniya ne ba: "Sun kware a dukkan bangarori na sararin samaniya. Suna da manufa ta siyasa da kuma kudin da za su cimma hakan."

Daya daga cikin manufofin China na zuwa duniya Wata ita ce ta samo wasu karafa daga can, wadanda suka hada da karfen lithium.

Sai dai Farfesa Sa'id Mosteshar, darakta a Cibiyar Nazarin Sararin Samaniya da Dokoko a Jami'ar London, ya ce China ba za ta ci riba sosai ba idan ta rika aikawa damutane duniyar Wata domin samo ma'adinai.

Karin bayanai daga Jeremy Howell da Tim Bowler