Abin da ya sa ƴan kasuwar Alaba Rago suka kai ƙarar gwamnatin jihar Lagos

Alaba Rago

Asalin hoton, others

Haɗakar ƙungiyoyin ƴan kasuwar Alaba Rago sun kai ƙarar gwamnatin jihar Legas gaban babbar kotun jihar.

'Yan kasuwar sun shigar da ƙarar ce don dakatar da gwamnatin jihar a shirinta na rusa ko korar su daga matsugunnin harkokin kasuwancinsu da ke Alaba-Rago.

Karar ta zo sakamakon barazanar da gwamnatin jihar ta yi na cewa za ta rushe babbar kasuwar cikin kwana 14.

Hukumomin jihar na zargin cewa masu aiikata ta'asa na samun mafaka a kasuwar - wani zargi da shugabannin kasuwar suka musanta.

Ƴan kasuwar sun nemi babbar kotun ta dakatar da hukumomin da abin ya shafa a shirin gwamnatin jihar Legas na rusa kasuwar, kowane lokaci daga gobe Talata 31 ga watan Mayun 2022.

A taron manema labarai da haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƴan kasuwar ta Alaba rago suka kira, sun bayyana cewa sun shigar da ƙarar ce a gaban babbar kotun jihar don takawa gwamnatin jihar da 'yan sanda birkin ɗaukar kowanne irin mataki da zai zama sanadin rasa ko lalata sana'oinsu.

'Yan kasuwar na cewa a maimakon gwamnati ta karɓe kasuwar, a shirye suke su gina irin ta zamani-wanda dama shi ne muradin gwamnatin Babajide Sanwo-Olu.

Alhaji Hussaini Muhammad Lajawa, shi ne shugaban kasuwar Alaba Rago, ya ce duk da sun shigar da ƙara a gaban kotu, hakan ba zai hana su ci gaba da tattaunawa da gwamnatin jihar don gano bakin zaren warware tsaka mai wuya da humomin jihar suke shirin jefa su ba.

"Muna da wannan yaƙini cewa kotu dai in Shaa Allah ƙarfi ce ga mara ƙarfi. Kuma idan ma wannan tattaunawar ba ta sauya wani abu ba, to za mu dangana da kotu don ƙwato mana haƙƙinmu.

"Gara a zauna a fahimci juna su gaya mana abin da suke so mu yi da mu ma wanda muke so a yi," in ji shi.

Wannan layi ne

Kasuwa mai ƙabilu daban-daban

Duk da cewa mutanen da suka fito daga arewacin kasar su ne suka ɗauki sama da kashi 70 cikin 100 na ƴan kasuwar, akwai kuma wasu ƙabilu da suka haɗa da Yarbawa da Igbo da sauran kabilu da ke hada-hadarsu cikin kasuwar.

Mr. Chibunna Onyirioba shi ne shugaban ƴan kasuwa da ke harkokin saye da sayarwa ta ɓangaren latironi a babbar kasuwar.

Ya ce: "Mu ba mu san inda suka samu waɗannan bukkoki ba. Hotunan da jami;an tsaron suka nuna wani yanki ne na jami;ar jihar Lagos, ba shi da nasaba da Kasuwarmu ta Alaba-Rago.

"Mun daɗe muna kira cewa a rushe wadannan wurare don gudun abin d aka je ya zo."

A ranar 17 bakwai ga watan Mayu ne dai wata tawagar ƴan sanda ta kai ziyara tare da kafa wata takarda ɗauke da umartar 'yan kasuwar ta Alaba Rago cewa su bar kasuwar cikin kwana 14 - wani lamari da ya tayar musu da hankali.

A ƴan makwannin baya ne dai wasu jami'an 'yan sanda da ke sintiri nesa da kasuwar Alabar suka gano makamai hannun wasu mutane a lokacin da suke bincike.

Bayan gano makaman ne wasu daga cikin mutanen da ake zargi suka tsere, kana suka shiga cikin kasuwar Alaba Rago- wani lamari da 'yan sanda suka yi zargin cewa ɓarayin na samu mafaka bayan sun aikata ba daidai ba ga mutane.

Sai dai Alhaji Hussaini Muhammad Lajawa ya ce babu ta yadda za su bai wa ɓarayi mafaka a babbar kasuwar.

Wannan layi ne

Kwankwaso ya ziyarci Alaba Rago

Kwankwaso

Asalin hoton, Kwankwaso Media Team

A yanzu dai shugabannin kasuwar ta Alaba Rago sun gana da sarkin Hausawan jihar Legas, Alhaji Aminu Yaro Dogara don ya yi amfani da ƙarfin fada a ji da yake da shi don tabbatar da kasuwar ba ta fita daga hannun 'yan arewacin Najeriyar ba.

A ziyarar da ya kai babbar kasuwar Alaba-Rago a ranar Lahadi, tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso, ya ce a shirye yake ya gana da gwamna da wakilan gwamnatin jihar Legas don tabbatar an dakatar da yunƙurin korar 'yan kasuwar.

Babbar kasuwar ta yi fice wajen saya da sayar da dabbobi da kuma ake iya samun kusan kowacce irin cimaka da suka haɗa da shinkafa da gero da dawa da masara da acca da maiwa da kaji da sauransu da akasari ake shiga da su daga arewacin Najeriya.

Alaba-Rago ta zama wata cibiya da kasashe da ke makwabtaka da Najeriya daga shiyyar kamar jamhuriyar Benin da Togo da Ghana da Jamhuriyar Nijar kan ci kasuwar sau bakwai a tsawon kowanne sati.

Ana faragabar cewa rusa kasuwar da maye gurbinta da wata sabuwa irin ta zamani na iya jefa dubun dubatar mutane rasa ayyuka da sana'o'insu kafin a kammala gina irin ta zamanin.

Wannan layi ne