Shekara ɗaya da mutuwar Abubukar Shekau: Munanan hare-hare 12 da Boko Haram ta kai da Najeriya ba za ta manta ba lokacinsa

Bayanan bidiyo, Bidiyo: Waiwaye kan munanan hare-haren da Shekau ya jagoranta a shekara 12

Shekara ɗaya bayan mutuwar shugaban ƙungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ana ta samun ƙaruwar ƴaƴan ƙungiyar da ke mika wuya ga sojojin Najeriyar.

Tun bayan mutuwar jagoran ƙungiyar ake ganin lagon ƙungoyar ya karye, kuma ruɗani ya kutsa cikinta, har wasu daga cikin ƴaƴanta da jigoginta suka shiga miƙa wuya ga sojojin Najeriya.

A ranar 19 ga watan Mayun 2021 ne aka fara samun labarin mutuwar Abubakar Shekau, mutumin da ya shafe shekara 12 yana jan ragamar kungiyar masu tayar da ƙayar baya ta Boko Haram, wacce ta dinga kai munanan hare-hare a Najeriya da Nijar da Kamaru har ma da Chadi.

Kafin lokacin mutuwar Shekau a watan Mayun 2021, a kalla sau hudu ana ba da rahoton mutuwarsa, amma yana fitowa yana ƙaryata hakan.

Tun da ya karɓi ragamar shugabantar ƙungiyar Boko Haram a shekarar 2009, ana yi wa Shekau kallon mara tausayi saboda yadda ya addabi al'ummar arewa maso gabashi, kai har ma da arewa maso yammaci da kuma arewa ta tsakiyar Najeriya, da ma wasu sassan, wadanda suka sa ya yi ƙaurin suna.

A yayin da yake cika shekara daya da barin duniya, BBC Hausa ta yi waiwaye kan wasu munanan hare-hare 12 da Shekau ya jagoranta cikin 12 da ya yi yana jan ragamar ƙungiyar, waɗanda suka daga hankula a duniya.

HARI NA ƊAYA

Police hqtrs bombing

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Harin da aka kai hedikwatar ƴan sanda ta Abuja shi ne na farko da Boko Haram ta kai babban birnin tarayya

Hari na farko da ya fara girgiza al'ummar Najeriya tare da daukar hankalin duniya da kungiyar ta yi karkashin shugabancin Shekau shi ne wanda ta kai hedikwatar 'yan sanda da ke Abuja ranar 16 ga Yunin 2011.

Duk da cewa mutum biyu ne suka mutu, amma ya tayar da hankali saboda ganin an shiga har birnin tarayyar Najeriya a karo na farko.

Short presentational grey line

HARI NA BIYU

Wata biyu bayan nan ne kungiyar ta sake kai wani harin bam a hedikwatar majalisar dinkin duniyar da ke Abuja babban birnin Najeriyar, inda akalla mutum 21 suka mutu.

Wannan shi ne lamari na biyu mafi muni da ya faru karkashin mulkin Shekau a ranar 27 ga Agustan 2011.

Short presentational grey line

HARI NA UKU

An kai wasu jerin hare-haren bam wasu coci-coci a Jos da Madalla a Suleja a ranar Kirsimetin shekarar 2011.

Sannan a wannan ranar an kai wasu hare-haren a Damaturu da Gadaka a jihar Yobe. Duk an samu asarar rayuka a lamurran.

Short presentational grey line

HARI NA HUƊU

Tabbas ƴan Najeriya ba za su taɓa mantawa da ranar 20 ga watan Janairun 2012 ba.

Rana ce da Boko Haram ta kai wasu jerin hare-hare a wurare daban-daban a lokaci guda a cibiyar kasuwancin arewacin Najeriya wato Kano, kuma rahotanni sun ce fiye da mutum 180 ne suka mutu.

A lokuta da dama idan Shekau ya bayar da umarnin kai munanan hare-hare, yakan bayyana a bidiyo ya shelanta abin da ya yi din.

A lokacin wadannan hare-hare na Kano ma aka ganshi a wani bidiyo yana cewa yana jin dadin kashe mutane - kamar yadda yake jin daɗin kashe kaji da raguna.

Short presentational grey line
Bayanan bidiyo, Waiwaye kan ƙungiyar Boko Haram yayin da ta cika shekara 10 da kafuwa
Short presentational grey line

HARI NA BIYAR

A ranar 16 ga Afrilun 2013 Boko Haram ta kai wani hari da ya sake daukar hankali a karo na biyar, wato na kisan-kiyashin garin Baga a jihar Borno, inda akalla mutum 187 suka mutu.

Bayan wannan ma, Baga ta sake ganin wani mummunan kisan-kiyashin a Janairun 2015 inda aka kashe mutum 150.

Short presentational grey line

HARI NA SHIDA

Mummunar aika-aika ta shida da Shekau ya bayar da umarnin aiwatarwa ita ce ta ranar 30 ga Fabrairun 2014 da mayakansa suka yi wa dalibai maza 'yan sakandaren gwamnatin tarayya ta Buni Yadi a jihar Yobe har 59 kisan-gilla.

Sun yi hakan ne ta hanyar harbe wasu da kuma yi wa wasu yankan-rago kamar yadda bayanai suka tabbatar.

Short presentational grey line

HARI NA BAKWAI

Shekau

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu sharhi sun ce Shekau ya ci karensa babu babbaka sossai ta hanyar uzzurawa ƴan Najeriya kafin ƙarshensa ya zo

A ranar 14 ga Afrilun shekarar 2014 din dai aka tayar da wasu bama-bamai biyu a tashar motar Nyanya a jihar Nasarawa, wajen da ke kusa da birnin tarayya Abuja inda mutum 88 suka mutu, kusan 200 kuma suka jikkata.

Short presentational grey line

HARI NA TAKWAS

Ga alama shekarar 2014 ita ta fi ganin manyan masifun da Shekaru ya jagoranta, saboda kwana daya kacal bayan harin Nyanya, sai aka wayi gari da labarin sace ƴan matan makarantar sakandaren Chibok a jihar Borno.

Wannan sata ita ce salon Shekau da ya fi jan hankali da kuma sake fitar da sunansa sosai a idon duniya.

Wani bidiyo da ya yaɗu da ke nuna shi yana dariya yana faɗar yadda zai sayar da ƴan matan ko ya aurar da su, ya nuna kowane irin mutum ne shi.

Mafi yawan ƴan matan sun tsira, kuma ga yaran da iyayensu da sauran mutane a yankin za su ci gaba da jin tasirin satar ko da a yanzu bayan mutuwar tasa.

Short presentational grey line

HARI NA TARA

Ran 2 ga Satumban 2014 kungiyar ta sake kai wani mummunan harin garin Bama a jihar Borno tare da kashe mutane da dama.

Wani dan majalisar dokoki daga jihar a wancan lokacin Ahmed Zanna ya shaida wa BBC cewa kwana 2 bayan aika-aikar, mayakan kungiyar sun hana a binne mutane.

Sannan daga baya gwamnati ta sanar da cewa Boko Haram ta kwace iko da Bama, kuma kusan mutum 26,000 ne suka zama ƴan gudun hijira.

Short presentational grey line

HARI NA 10

Ranar 28 Nuwamban 2014 ƙungiyar ta sake kai wani mummunan hari a babban masallacin Juma'a na cikin birnin Kano da ke kusa da gidan sarki.

A ƙalla mutane 120 masu Sallar Juma'a ne suka rasa rayukansu, wannan shi ne hari na goma cikin jerin wadanda suka daga hankulan jama'a.

Short presentational grey line

HARI NA 11

Ranar 9 Disambar 2016 aka tayar da bama-bamai biyu a Madagali da ke jihar Adamawa, inda mutum 57 suka mutu sannan 177 suka jikkata.

Short presentational grey line

HARI NA 12

Zabarmari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gwamna Zulum ne ya jagoranci sallar jana'izarsu

Hari na 12 mafi firgitarwa shi ne wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce an kashe kimanin mutum 110 a harin da ƴan Boko Haram suka kai wa manoma kusa da garin Maiduguri a watan Nuwamban 2020.

Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno shi ya jagoranci jana'izar mutanen da Boko Haram ta yi wa yankan ragon a Zabarmari da ke Ƙaramar Hukumar Mafa a jihar.

Short presentational grey line

A yanzu dai masu sharhi na ganin mutuwar Shekau ta rage ƙarfin da ƙungiyar ke da shi, sai dai har abada ba za a manta halin ƙunci da wahalar da ayyukansa na kashe-kashe da satar mutane suka jefa al'umma ba.

Sai dai duk da waɗannan munanan ayyuka da Shekau ya aikata, su ma sojojin Najeriya da Nijar da Chadi da na Kamaru, sun sha samun nasara a kansa da mayakansa.

Kuma a ƙarshe a iya cewa al'ummomin wadannan kasashe hudu suke da nasara, ta ganin bayan wannan dan ta da kayar bayan, wanda a karshe ma rahotanni sun ce shi ya kashe kansa da kansa.

Wannan layi ne