Abubakar Shekau: Waiwaye kan mutumin da ya addabi 'yan Najeriya cikin shekaru goma

Asalin hoton, AFP
Jerin munanan abubuwan da Abubakar Shekau ya jagoranci yi suna da yawa, amma sace ƴan mata ɗalibai na makarantar sakandaren Chibok kusan 300 a Najeriya ne ya sa ya yi ƙaurin suna.
Tun bayan da ya karɓi ragamar shugabantar ƙungiyar Boko Haram a shekarar 2009, Shekau ya zama mara imani da tausayi da ya addabi al'ummar arewa maso gabashin Najeriya da ma na wasu sassan.
A shekarar 2014, sai tasirin Boko Haram ya sauya bayan da mayaƙan ƙungiyar suka kai hari makarantar Chibok.
Fafutukar ceto ƴan matan da aka ƙaddamar mai take "Bring Back Our Girls" ta ja habkalin duniya tare da fitar da labarin, amma kuma shi ma Shekau sunansa ya fito sosai a idon duniya.
Wani bidiyo da ya yaɗu da ke nuna shi yana dariya yana faɗar yadda zai sayar da ƴan matan ko ya aurar da su, ya nuna kowane irin mutum ne shi.
Mafi yawan ƴan matan sun tsira. Wasu kuwa har yanzu suna tsare a hannun ƴan Boko Haram, kuma ga yaran da iyayensu da sauran mutane a yankin za su ci gaba da jin tasirin satar ko da bayan mutuwarsa.
Ana ganin Shekau, wanda shi ne aka fi nema ruwa a jallo a Najeriya, a matsayin mara tsoro da ke rayuwa a killace, mai murɗaɗɗen hali, mai halin hawainiya, mai da'awar sanin addini kuma ɗan daba.

Asalin hoton, AFP
An haifi Abubakar Muhammad Shekau wanda mabiyansa ke kira imamu, wato shugaba ko jagora, a ƙauyen Shekau da ke jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya.
Wasu na cewa shekarunsa sun kusa 40, yayin da wasu kuma suke cewa ya haura 40 - wani abu da babu tabbas a kai da ke cikin sirrukan da har yanzu ba a gama sani ba dangane da shi.
Ɗalibin addini mai tsananin son kawo sauyi
A shekarar 2009 an ruwaito cewa dakarun tsaro sun kashe shi - kawai sai ga shi ƙasa da shekara ɗaya ya sake bayyana a wasu bidiyo da aka wallafa a intanet ana gabatar da shi a matsayin sabon shugaban ƙungiyar Boko Haram.
Daga baya an sha ƙara samun rahotannin mutuwarsa amma daga baya aka gano duk ƙarya ne.
Gwamnatin Amurka ta yi tayin tukwicin dala miliyan bakwai don samo bayanai kan inda yake, amma ba a ta ba dacewa da gano inda yake ɓuya ba.
Muhammad Yusuf wanda shi ne ya ƙirƙiri ƙungiyar Boko Haram, ya mutu a hannun ƴan sanda a watan Yulin 2009, sannan an kashe ɗaruruwan mutane a ba-ta-kashin da aka yi bayan nan - inda mutane da dama suka yi zargin cewa wannan lamarin ne ya sa ƙungiyar ta zafafa kai hare-hare.
An ce wani mai suna Mamman Nur, wanda shi ma ake nemansa ruwa a jallo saboda kitsa kai wani harin bam, shi ya kai Shekau wajen Muhammad Yusuf ya gabatar da shi.

Dukkansu su ukun ɗaliban addini ne kamar yadda suke kiran kansu - kuma an fi ganin Shekau a shiru-shirun cikinsu amma kuma mai tsattsaurar aƙida.
"Bai faye magana ba, ba shi da tsoro," a cewar Ahmed Salkida, wani ɗan jarida da ke mu'amala da Boko Haram, wanda akwai lokacin ma da aka yi zargin shi ɗaya daga cinkinsu ne.
"Yana ɗaya daga cikin waɗanda suka yi amannar cewa za ka iya sadaukar da komai naka a kan abin da ka yi imani da shi," in ji Salkida.
Shekau da Nur sun ci gaba da jan ragamar ƙungiyar bayan mutuwar Yusuf amma daga baya sun samu saɓanin fahimta a kan abubuwa da dama, al'amarin da ya jawo darewa ƙungiyar gida biyu.
Nur da sauran manyan kwamandojin sun yi ta sukar salon mulkin Shekau don haka suka ɓalle a shekarar 2016, a cewar ƙungiyar a International Crisis Group.
Ɓangaren Nur wanda Abu Musab al-Barnawi, ɗan Mohammed Yusuf ke jagoranta, ya haɗa kai da ƙungiyar Islamic State inda ya ɗauki sunan Islamic State a Yankin Afirka Ta Yamma wato (Iswap).
Iswap ta zargi Shekau da aikata laifuka da dama da suka haɗa da take dokokin Musulunci sannan a watan Yunin 2018, ta ce Shekau "annoba" ce da ya kamata a kawar.
An ruwaito cewa an kashe Nur a watan Agustan 2018, kuma wasu abokansa a Iswap ne suka aikata hakan bayan saɓanin da suka samu kan wasu "akidoji masu sauƙi."

Boko Haram ataƙaice:
- An kafa ta a shekarar 2002
- Da farko tana adawa ne da ilimin boko
- Ta ƙaddamar da hare-hare a shekarar 2009
- Ta ja hankalin duniya a shekarar 2014 bayan sace ƴan matan Chibok
- Ta ɓlle biyu a shekarar 2016

Shekau yana jin yaren barbarci sosai sannan ya iya Hausa da Larabci. Ya kan jefa kalmomin Turanci a wasu saƙonninsa da ake naɗa da yake aike wa yan jarida.
A yayin da aka kashe Muhammad Yusuf, an ce Shekau ya auri ɗaya daga cikin matansa huɗu ya kuma karɓi riƙon ƴaƴansu - mai yiwuwa don kare martabar tsohon shugabansa kamar yadda wasu majiyoyi da ba sa so a ambaci sunayensu suka faɗa.
Shekau ba ya magana kai tsaye da mayaƙan ƙungiyar - ya kan yi nu'amala ne da wasu tsirarun jagororin ƙungiyar, amma ko su ɗin ma ba kasafai yake tuntuɓarsu ba.
Salkida ya ce "mafi yawan masu kiran kansu shugabanni a ƙungiyar ma ba sa tuntuɓarsa kai tsaye."
Shekau ba shi da kwarjini sannan ba shi da fasahar iya tsara zance kamar na Muhammad Yusuf - amma yana da tsattsaurar aƙida da rashin imani, in ji mutanen da suka fahimci ƙungiyar da kyau.
Ya fitar da saƙo a ɗaya daga cikin bidiyonsa wanda ya bayar da haske kan tsarin shugabancinsa.
"Ina jin dadin kashe duk wanda Allah Ya ba ni umarnin kashewa - kamar yadda nake jin daɗin kashe kaji da raguna," kamar yadda ya faɗa a wani bidiyo da aka saki jim kaɗan bayan da Boko Haram ta kai ɗaya daga cikin hare-harenta masu muni a watan Janairun 20212, inda fiye da mutum 180 suka mutu a Kano, birni mafi girma a arewacin Najeriya.

Asalin hoton, AFP
Shekau shi ne kuma jagoran addini na ƙungiyar, an sha ganinsa a bidyyo yana yi wa mabiyansa wa'azi ko huɗuba.
"Yana da ƙarfin hadda sannan yana da sani a addini," a cewar Salkida.
Mabiyansa kan ira shi da "Darul Tawheed", wato wanda ya ƙware a fannin Tawheed na kaɗaita Allah, wani ilimi mai muhimmanci a Musulunci.
Amma manyan malaman addinin Musulunci na Najeriya ba sa ɗaukar Shekau a matsayin malami kuma suna ƙalubalantar salonsa na fahimtar addini.
Suna yawan yin Allah-wadai da hare-haren da mabiyansa ke kaiwa kan duk wanda bai yarda da aƙidarsu ba, ciki kuwa har da Musulmai.
A yanzu dai, mutuwar Shekau za ta rage ƙarfin da ƙungiyar ke da shi amma har yanzu za ta iya kai hare-hare, sannan an kasa murƙushe ta duk da irin fafutukar da sojoji ke cewa suna yi.
Sai dai har abada ba za a manta halin ƙunci da wahalar da ayyukansa na kashe-kashe da satar mutane ya jefa al'umma ba.











