Zabukan Lebanon: Matasan da suka sha alwashin rama abin da ‘yan siyasa ke musu

Lebanese expats dance as they queue to cast their votes for 15 May legislative election at Lebanon's Consulate in the Gulf emirate of Dubai on May 8, 2022.

Asalin hoton, Getty

Masu kada kuri'a za su fita zuwa rumfunan zaben a ranar Lahadi 15 ga wata don zabar 'yan majalisar dokokin kasar 128.

Shi ne zabe na farko da za a gudanar tun bayan gagarumar zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati a shekarar 2019 da kuma mummunar fashewar da ta faru a tashar jiragen ruwa a shekarar 2020 - duka abubuwan biyu ne da suka kara karfin yin kira da a kawo sauyin siyasa.

Hakan ne ya sa wasu matasa masu fafutika suka yi kira ga masu kada kuri'a da su dauki ''fansarsu'' a akwatunan zabe kan 'yan siysar da suke yi wa kallon wadanda suka bari kasar ta fada cikin mawuyacin halin da aka shiga.

Amma mene ne muhimman batutuwa gabanin zaben na ranar Lahadi?

Matsin tattalin arziki

Tushen abin shi ne daya daga cikin tsananin matsin tattalin arziki mafi muni a duniya da ko wace kasa za ta fuskanta tun a cikin shekarar 1850, a cewar Bankin Duniya.

"Mutane da dana na yin aiki uku, ko hudu ko biyar don kawai su samu wadataccen abubuwan rayuwar yau da kullum,'' in ji Nathalie Abou Harb mai shekaru 23, wata mai fafutika a birnin Beirut wacce a karon farko ne za ta kada kuri'a.

"Mafi karancin albashi a yanzu shi ne lira 800,000 na kasar Lebanon, a yayin da kudin tankin gas daya ya kama lira 500,000.

Don haka idan kana samun mafi karancin albashi ne, ba za ka iya cika tankin motarka da mai sau biyu ba.''

A woman leaves a bakery with a bag of bread as people wait for their turn, in the neighbourhood of Nabaa in the Lebanese capital Beirut's southern suburbs, on August 13, 2021,

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yan Labanon na cikin matsin tattalin arziki

Tun ma kafin barkewar annobar korona, tattalin arzikin Lebanon yana tangal-tangal ne.

Kusan daya bisa ukun yawan al'ummar kasar na rayuwa ne cikin kangin talauci, rashin aikin yi ya kai kashi 25 bisa dari kana kasar na ta fadi tashi da durkushewar tattalin arziki, da karuwar hauhawar farashin kayayyaki, kamar yadda wani bincike da Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF) ya nuna a watan Oktobar shekarar ta 2019.

Gwamnati na cikin kangin basussuka masu tarin yawa, da kuma karancin kudin da za ta gudanar da ayyukan raya al'umma.

Mutane da dama na kara fusata da bakin ciki game da gazawar gwamnati wajen samar da ko da kananan ababuwan more rayuwa.

Suna fama da yawan daukewar wutar lantarki a kullum, da karancin tsaftataccen ruwan sha, da karancin kiwon lafiya, da rashin kyawun hanyoyin sadarwa na intanet.

Zanga-zangar shekarar 2019

A watan Oktobar 2019, wani shirin kara yawan kudin haraji a kan makamashi da kuma da samar da hanyoyin sadarwa na sakon murya ta intanet kamar su WhatsApp, sun kara rura wutar zanga-zanga a kan tafiyar da harkokin tattalin arziki, da cin hanci da rashawa, da wasu fitattun 'yan siyasa na gargajiya.

Hakan ya haifar da yin murabus din gwamnati.

Amma kamar yadda daya daga cikin manyan jaridun kasar Lebanon L'Orient-Le Jour, ta yi nuni, zanga-zangar ba kawai saboda harajin ''WhatsApp tax" kadai ba ne.

Mutane sun fusata, ta ce, saboda shafe ''shekaru da dama na rashin alkinta basussuka, da tattalin arziki da rashin tabuka komai na farfado da tattalin arziki a kan matsalolin yau da kullum.

"Mutane a fadin Lebanon na bukatar yi wa jama'a adalci a fannonin hakkin biladama da ilimi, da kiwon lafiya da kuma aiki,''

Lebanese riot police react to fireworks thrown by supporters of Lebanon's Shiite Hezbollah and Amal groups during clashes on December 14, 2019 in central Beirut.

Asalin hoton, Getty Images

Da dama na zargin fitattun masu mulki da suka kankane harkokin siyasa na tsawon shekaru kana wadanda mutane suka yi amanna sun azurta kan su a yayin da suka gaza yin wasu sauye-sauyen da suka kamata wajen shawo kan matsalolin da kasar ke fuskanta.

Annobar korona ta kara munin al'amura ta hanyar tilasata wa tattalin arzikin tsayawa ciki tare da haddasa wa harkokin yawon bude ido yin kasa zuwa kashi 70 bisa dari kamar yadda Kungiyar Kamfanonin Lura da Harkokin Yawon Bude Ido ta kasar ta bayyana.

A lokacin da harkokin kasuwanci suka dawo a shekarar 2021, kudin kasar da darajarsa ta karye ya haddasa tsadar shigo da kayan abinci, da makamashi da magunguna, tare da haddasa hauhawar farashin kayyyaki da matsanancin karancinsu.

Doyagen layuka sun karu a gidajen mai, da wurin masu sayar da gas din girki da gidajen gasa burodi, saboda karancin wutar lantarki sun haddasa tsadar sarrafawa da kuma yadda suke iya gasa burodin.

Nathalie ta bayyana cewa wadannan matsaloli har yanzu na nan, kana wasu kayayyakin da ake amfani da su yau da kullum sun yi karanci ko kuma tsananin tsada''.

"Har yanzu ana biyan mutane matalauta da kudin lira na Lebanon, wanda darajarsa ta karye, a yayin da ake biyan masu kudi da dalar Amurka, ko suna samun dalar daga waje. Babu sauran wasu mutane masu matsakaicin sami,'' ta ce.

Fashewa a tashar jiragen ruwa ta Beirut

A ranar 4 ga watan Agustar shekarar 2020, wani jirgin ruwan dakon kaya makare da sinadarin ammonium nitrate ya fashe a Tashar Ruwan Beirut, tare da hallaka akalla mutane 218, da kuma jikkata mutane sama da 7,000.

Mutane da dana sun fusata a lokacin da suka fahimci cewa an ajiye sama da tan 2,000 na sinadarin mai cike da hadari a babban dakin ajiyar kayayyaki har na tsawon shekaru shida, bayan da aka kwace daga wani jirgin ruwa.

An ji karar fashewar daga nisan kilomita 240 daga kasashe makwabta. Mutane fiye da 300,000 ne suka rasa gidajensu.

Kungiyoyin kare hakkin biladama kamar Amnesty International sun zargi mahukuntan da ''rashin nuna dattaku wajen toshewa wadanda hadarin ya shafa hanyoyin neman a yi musu adalci,''

An aerial view taken on August 7, 2020, shows a partial view of the port of Beirut and the crater caused by the colossal explosion

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A watan Agustan 2020 ne aka samu fashewar da ta daga hankalin duniya a Labanon

Sakamakon da ya biyo bayan wannan matsala shi ne durkushewar tattalin arziki.

Daga dala bilyan 52 a shekarar 2019, an kididdige alkaluman irin kayan da kasar Lebanon ke samarwa da GDP yin kasa zuwa dala biliyan 21 da milyan takwas a shekarar 2021 - subutowa kasa zuwa kashi 60 bisa dari.

"Galibi a kan danganta irin wadannan mummunar raguwa da tashe-tashen hankula na yake-yake,'' masana tattalin arziki na Bankin Duniya suka bayyana a makalar sa ido kan tattalin arziki da aka wallafa a shekarar 2021.

Fiye da rabin yawan al'ummar kasar na miliyan shida da dubu dari takwas - da suka hada da 'yan gudun hijirar kasar Syria - aka kididdige cewa ke fama da matsanancin talauci.

Rashin ɗaukar mataki a siyasance

Wadannan abubuwa sun kara haifar da yin kira ga a kawo sauyin siyasa - a ciki da wajen kasar.

Tun a lokacin zanga-zangar watan Oktoban shekarar 2019, kungiyoyi da jam'iyun siyasa da dama ne suka bayyana tare da yin alwashin "shiga majalisar dokokin Lebanon da yin la'akari da batun juyin-juya halin 17 ga watan Oktobar shekarar 2019".

"Wadannan jam'iyun siyasa ne da suka kasance a cikin gwamnati kana da suka mulki gwamnati har na tsawon shekaru 50, sun samu damammakinsu na cika alkawuran da suka yi. Dole su amince cewa sun gaza,'' Nathalie ta yi amanna.

Kwararru sun ce matsalolin siysar Lebanon sune tsarin siyasarta na siyasa hade da addini. Hakan na nufin ana bai wa al'ummar addinai wani kaso na kujeru a bisa yanayin yawan al'ummarsu.

Tsarin wanda aka yi shi don gyara banbance-banbancen akida, ya haifar da yawan cin hanci da rashawa kamar yadda kungiyar Transparency International ta bayyana.

Ghia Assaad, daga kungiyar adawa Liqaa Tishreen, ya bayyana cewa sabbin jam'iyun a karon farko na bukatar kungiyar ba da ruwanta da irin wannan tsari na wake da shinkafa su shiga majalisar dokokin.''

Nathalie ta ce: "Zuwan sabbin jam'iyun siyasa da kungiyoyin adawa yan una cewa yanzu mutane bas a bukatar rarrabuwar kawuna. [Wannan tsarin] ya zama tsohon yayi kana lokaci ya yi da za a kawo sauyi.''

Activists and relatives of victims of the Beirut port explosion scuffle among themselves as Lebanese security members try to interfere during a demonstration on September 29, 2021 outside the capital's Justice Palace

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dangin mutanen da suka mutu a fashewar da ta faru a Beirut sun shiga damuwa kan gazawar da suke ganin gwamnati ta yi

Kuri'ar matasa

Sabbin jam'iyun sun yi kira ga matsa da su kada kuri'a, musamman ma dubban matasan da suka bar kasae sakamakon matsin tattalin arzikin baya-bayan nan.

Mutane fiye da 225,000 ne suka yi rijistar kada kuri'a a wannan zabe daga kasashen waje, linki uku a kan na shekarar 2018.

Fiye da 130,000 suka yi haka a kasashen 50, kamar yadda alkaluman kiddidiga na hukuma suka bayyana, inda aka samu alkaluma mafi yawa na sama da kashi 70 bisa dari a Hadaddiyar Daular Larabawa.

"Matasa sun farga cewa iyayensu da kakannninsu ba su yi zabin siyasa mai kyau ba. Don haka sun dauki nauyin kawo sauyi,'' Nathalie ta bayyana.

"Suna son su dauki fansa: fansa a kan mutanen da ya kamata a dora wa laifi kan fashewar Beirut da suka bari kasar ta fada cikin matsin tattalin arziki, wadanda suka sa muke tsayawa kan dogayen layuka a gaban gidajen mai, da na gas da shaguna da kuma gidajen burodi.''

Kuri'un mazauna kasashen wajen kashi 6 bisa dari ne kacal na yawan wadanda suka yi rajistar a kasar Lebanon (miliyan 3 da dubu dari bakwai) amma Nathalie ta yi amanna zai wadatar wajen samun galabar kujerun da za su sa sabbin jini shiga majalisar dokokin.

"Mun san cewa ba za mu iya, ba zamu sauya duka wakilan ba a wadannan zabukan. Watakila ba za mu iya sauya fiye da mutane goma ba a majalisar,'' ta ce.

"Amma hakan ba wai game da sauya abubuwa a yanzu ba ne. Mutane na neman yadda za sus amu babbar hanya da kuma tunanin makomarsu da ta 'yayansu.''

line
A Lebanese woman displays her ink-stained finger after voting at the Lebanese embassy in Riyadh during parliamentary elections on May 6, 2022

Asalin hoton, Getty Images

Ta yaya tsarin siyasar Lebanon ke aiki?

A hukumance Lebanon ta amince da al'ummar addinai 18 - Musulmai hudu, Kiristoci 12, masu akidar Druze da Judaism 12.

An kasafta kujerun majalisar dokokin 128 tsakanin Kiristoci da Musulmai ( da suka hada da masu akidarDruze).

Manyan mukaman siyasa uku - shugaban kasa, da kakakin majalisar dokoki da firaminista - an kasafta a tsakanin al'ummomin (Kirsita dan darikar Maronite; Musulmi dan Shia; da Musulmi dan Sunni) a karkashin yarjejeniyar da aka yi a baya cikin shekarar 1943.

Wannan salon mulki na gamayyar addinai ne ta sa kasar ta kasance mai sauki ga manyan kasashe wajen yin katsalandan, kamar yadda aka shaida a yadda kasar Iran ke mara wa kungiyar 'yan Shia ta Hezbollah, wacce a tarihi a ke mata kallon daya daga cikin kungiyar siyasa da soji mafi girma a kasar Lebanon.

Kasar Saudiyya, kasa 'yar Sunni mafi girma a Yankin Gabas ta Tsakiya ita ma ana yi mata kallon wacce ke da karfin fada a ji a kan siyasar kasar Lebanon.

Tun bayan kawo karshen yakin basasa, shugabannin siyasa daga ko wace darika sun ci gaba da rike matsayinsu ta hanyar wannan tsari - suna kare muradun al'ummomin addinansu da suke wakilta, tare da samar da tallafin kudaden abubuwan more rayuwa ta hanyar da ke bisa ka'ida da kuma akasin haka.

Sabuwar majalisar dokokin za ta zabi sabon shugaba bayan Michel Aoun, daga jam'iyar Kiristoci ta Christian Free Patriotic Movement, ya kammala wa'adinsa a cikin watan Oktoba.

A cikin watan Janairu, tsohon firaminstan Sunni, Saad Hariri ya sanar da cewa jam'iyarsa ta Future Movement ba za ta fitar da dan takara ba a zabukan 'yan majalisar dokoki na ranar Lahadi.

Bayan yanke shawarar da Hariri ya yi, kwararrun na fargabar rashin 'yan Sunni a cikin siyasar kasar Lebanon ko yiwuwar karuwar karfin kungiyar Shia ta Hezbolla wacce ke samun goyon ayan kasar Iran.