Daga abota zuwa tashin hankali: Wane hadari ake ciki a Koriya ta Arewa?

Kim Jong Un da shugaba Yoon Suk-yeol
    • Marubuci, Daga Jean Mackenzie
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC a Seoul

Kim Jong-un na gwajin makamai masu linzami a Koriya ta Arewa cikin gaggawa, a daidai lokacin da Koriya ta Kudu ke shirin rantsar da sabon shugaba mai halin ba sani ba sabo.

Bayan rashin nasarar gwajin makami mai linzami a shekarar da ta gabata, sai kuma ga sabon tahin hankali na ƙara ɓulla a yankin.

"Na fara tunanin ɗauko gatari, amma sai na fahimci zai yi nauyin ɗauka, sai na yanke shawarar ɗaukar wuƙa."

Jenn na zaune a wata mashaya maras hasken wutar lantarki, da tsakar dare, ta tuna abin da ya faru da ita lokacin da ta shirya tserewa.

A matsayinta na 'yar Koriya ta Kudu, mazauniyar birnin Seoul, tsaf ta san abin da zai faru idan makwabciyarsu Arewa ta kawo hari.

Abu na farko da ta tanada su ne makamai, sai kuma babura biyu, ɗaya nata ɗayan kuma na ɗan uwanta. Za su goya iyayensu a baya.

Ta haka ne za su iya tsallaka kogin birnin cikin gaggawa, kafin Koriya Arewa ta fara ruwan makamai da bama-baman da za su lalata gadar, da fatan ƙarasawa gaɓar teku kafin ita ma ta fuskanci fushin bama-baman.

Wata rana ita da ɗan uwanta suka zana taswirar hanyoyin da za su bi wajen tserewa, sun amince su ɗaura ƙyalle a jikin bishiyoyi yadda za su iya gane hanya ko da sun rabu.

Wannan ya faru shekaru biyar da suka gabata. A lokacin, Koriya ta Arewa na ta gwajin makamai masu linzami cikin fushi, da ƙoƙarin harba bama-bama nukiliya zuwa Amurka, kuma Shugaba Donald Trump na barazanar mayar da mummunan martanin da ya kira "luguden wuta" kan Arewar.

Jenn ta amince ta damu matuƙa. Amma duk da haka, wannan kaɗan ne daga cikin halin da Koriya ta Kudu ke ciki, suna cike da fargaba kan ko za su ƙara faɗawa yaƙi da maƙwabciyarsu bayan shekaru 70 da suka gabata.

Kwatsam sai wani abu ya faru. Sabon shugaban Koriya ta Kudu da aka zaba a lokacin, Moon Jae-in, ya shawo kan Mista Trump kan su gana da Kim Jong-un.

Shi ne karon farko da wani shugaban Amurka ya taba ganawa da shugaban Koriya ta Arewa.

Lamari ne mai cike da tarihi, haduwar shugabannin biyu a taron koli, ya ɗarsa wani fata a zuƙata, ta yiwu Arewa ta amince da jingine batun kera makaman nukiliyarta, hakan zai kawo zaman lafiya tsakanin kasashen kuma maƙwabtan juna.

Shugaba Trump da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un, jim kadan bayan haduwarsu a cibiyar lalata makaman nukiliyar Arewa (DMZ) - dukkan shugabannin sun ce za su tabbatar da kammala lalata cibiyar makamin nukiliya daga yankin Koriya baki daya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Trump da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un, jim kadan bayan haduwarsu a cibiyar lalata makaman nukiliyar Arewa

Zakwaɗi da ɗoki sun cika Moon, wanda ɗa ne ga 'yan gudun hijirar Koriya ta Arewa, da suka isa babban birnin kasar Pyongyang tare da shiga dandalin wasanni, sun sha hannu da juna.

Dandazon mutanen da ke wajen ba su san abin da za su yi ba, kamar yadda Farfesa Moon Chung-in ya tuna, wanda shi ne mai ba shugaban shawara a lokacin.

An shaida musu wanna mutumin babban maƙiyinsa ne, sai kuma ga shi a ƙasarsu yana batun zaman lafiya. Jim kaɗan da sama da 'yan Koriya ta Arewa 150,000 suka fara tafa hannu raf-raf-raf babu ƙaƙƙautawa.

"Abin mamaki ne da al'ajabi, gwanin dadi da mu na kallo, lamari ne na ci gaba," in ji shi.

Dandazon 'yan Koriya ta Arewa lokacin da suke yi wa shugaba Moon Jae-in lokacin da ya ke yi musu jawabi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dandazon 'yan Koriya ta Arewa lokacin da suke yi wa shugaba Moon Jae-in lokacin da ya ke yi musu jawabi

Amma Shugaba Moon na barin ofis, dan fatan da ake da shi na zaman lafiya ya bi rariya. A lokacin da yarjejeniyar nukiliya tsakanin Amirka da Koriya ta Arewa ta bi shanun sarki a shekarar 2019, haka ma tattaunawar zaman lafiya tsakanin kasashen Koriya ta zo karshe.

Tun daga lokacin ake zaman doya da man ja tsakanin kasashen. A bangare guda kuma Koriya ta Arewa ta ci gaba da ƙera makaman nukiliyarta, da kuma gwajinsu ba tare da ƙaƙƙautawa ba cikin tsageranci da nuna isa da halin ko in kula.

A wannan lokacin ne, annobar korona ta ɓulla, sai kuma yakin Ukraine da Rasha na baya-bayan nan, lamarin ya nuna idanun duniya sun kau daga yankin, sun koma wani wuri na daban.

An tambayi ko gwamnati ta gaza, amma Farfesa Moon Chung-in ya kare wannan da cewa. "A'a, ba na jin haka ne! Akwai yaƙi ne?" Ya kare matakin da cewa shekara biyar gwamnatin Moon ta yi ta tabbatar da zaman lafiya, a lokacin daya daga cikin rigimar sasantawa mafi girma.

Ya kuma yi kokarin komawa teburin sulhu tsakanin kasashen biyu. Ya ce ya yi amanna matsalar ita ce masu shiga tsakani na bangaren Koriya ta Arewa sun sake komawa tattaunawar hannu rabbana, a abin da ya kira babban abin kunya ga gwamnatinsu, kuma lamarin da ba lallai a hukunta su da aikatawa ba.

Shugaba Moon ya yi duk kokarin da zai yi domin ganin an sake komawa sulhu da Koriya ta Arewa, amma a karshe sai da aka yi zarginsa kan lalashin shugaban da ak wa kallon mafi tsageranci da zalunci a duniya.

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un (na 2 a hagu) da matar shi Ri Sol Ju (hagu) sun dauki hoto tare da shugaba Moon Jae-in (na biyu a dama) tare da matar Kim Jung-sook (dama) a saman tsaunin Paektu a 20 watan Satumba , 2018 a tsaunin Paektu, da ke Koriya ta Arewa. (Photo by Pyeongyang Press Corps/Pool/Getty Images)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kim Jong-un da shugaba Moon Jae-in sun gana sau uku a shekarar 2018

Hanna Song ta tuna abin da ta ji a wancan lokacin shekaru biyar da suka wuce.

"Lokacin da na ga hotunan da suka dauka, rike da kafadun juna su na dariya, fuskokinsu cike da annashuwa, sai da wani sanyi ya tsarga min tun daga sama har kasa," a lokacin da take magana a ofishinta da ke Seoul.

Ita ce shugabar cibiyar ƙididdiga a hukumar kare hakkin dan adam ta Koriya ta Arewa, suke bin diddigin laifukan take hakkin dan adam a Koriya ta Arewa sama da shekara 20. Ta ce shekarun da suka gabata lamarin ba mai sauki ba ne.

Hanna ta ce batun hakkin dan adam, shi ne abin da Kim Jong-un ba ya kauna sam. Ta ce a kokarin da ake yi na sanya shugaba Kim ya sake a sasantawar, sai Shugaba Moon ya kawar da wannan batun.

Hanna Song ta yi amanna an rasa manyan shaidu kan cin zarafin dan adam

Asalin hoton, BBC/Hosu Lee

Bayanan hoto, Hanna Song ta yi amanna an rasa manyan shaidu kan cin zarafin dan adam

Kungiyarsu Hanna ta tattauna da wadanda suka tsere daga Koriya ta Kudu, a cibiyar Hanawon da suka fara zama na watanni uku.

Labaran da suka bayar sun taka muhimmiyar rawa wajen samun bayanan take hakkin dan adam. Amma shekaru biyu da suka wuce, gwamnatin Koriya ta Kudu ta datse duk wata hanya da za a samu damar zuwa cibiyar ko magana da mutane, hakan na nufin komai ya bata.

Daga nan Hanna ta fara samun labari daga wadanda suka tsere, cewa an takura musu kan kada su kuskura su yi magana da kowa kan halin da suka samu kan su a ciki lokacin da suke cibiyar da ke Koriya ta Arewa.

Wasu daga ciki 'yan sandan yankunan sun kira tare da sanya musu na'urar da ke nadar kowanne motsi da za su yi. "Kun tabbatar hakan ya dace?" suka tambaya.

Hanna ta yi kokarin kalubalantar gwamnati, kan ɓatan-dabon bayanan. "Me za ka yi idan ba ka samu wani bayani ba, saboda kawai ku na son tabbatar da Kim Jong-un bai ji kunya a idon al'umma ba?" abin da ta tambaya kenan, ba kuma tare da samun wata amsa ba.

"Abin da ke faruwa a Ukraine na da tayar da hankali," Hanna ta karkare da cewa, "ko ba komai dai mun sani."

Kim Jong-un a gaban babban makami mai cin dogon zango da aka sa ni Koriya ta Arewa ta kera

Asalin hoton, KCNA

Bayanan hoto, Kim Jong-un a gaban babban makami mai cin dogon zango da aka sa ni Koriya ta Arewa ta kera

Sai dai rungumar juna, ta musabaha da juna ta zo karshe. Koriya ta Kudu ta zabi sabon shugaban kasa, wanda ake ganin mai tsauri ne, tsohon mai gabatar da kara na gwamnati, wanda babu ruwan shi da 'yan siyasa kuma bai kware a fannin ba.

A tattaunawarsa ta baya-bayan nan Yoon Suk-yeol ya bayyana Koriya ta Arewa da cewa "babbar maƙiyiya ce" ga Koriya ta Kudu, ya kuma yi alkawarin daukar matakin ba sani-ba-sabo tsakaninsu.

Ya ce zai amince ya yi magana da makofciyarsa idan ya ga cewa da gaske ta ke kan shirin lalata cibiyar makamin nukiliyarta. Sai dai kwararru sun amince Arewa ba ta da aniyar kawo kasrshen nukiliyar.

An cimma hakan ne gabannin yakin da aka fara a Ukraine inda ya yi karin haske kan makamai irin wannan, duk da cewa babu wani taimako da hakan ya yi.

Hakan ya bai wa Mista Moon hasken babu wani sauyi, kamar tadda wani kwararre Chris Green kan harkokin kasashe a cibiyar da ke kare afkuwar yaƙe-yaƙe.

Sabon shugaban Koriya ta Arewa Yoon Suk-yeol ya yi alkawarin daukar tsattsauran mataki kan Koriya ta Arewa

Asalin hoton, News1

Bayanan hoto, Sabon shugaban Koriya ta Arewa Yoon Suk-yeol ya yi alkawarin daukar tsattsauran mataki kan Koriya ta Arewa

A lokacin gangamin yakin neman zabe, Mr Yoon ya ce zai kaddamar da hare-hare masu tsada ga Koriya ta Arewa, matukar ya samu labarin ta na shirin kawo mata hari.

Wannan ya dade yana cikin ajandar ma'aikatar tsaron Kudu, sai dai hakan ba ta faru ba.

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya jagoranci faretin soji a birnin Pyongyang a watan Afirilu

Asalin hoton, KCNA

Bayanan hoto, Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya jagoranci faretin soji a birnin Pyongyang a watan Afirilu

Zaune a wurin cin abinci, suna cin gasasshen nama, a wani wurin shakatawa da ke Seoul, Lee Geon-il ya gyara gilashin idonsa, ya kalli abokinsa da ke cin wani nauyin gashin nama da barasa, "Yaya ne, ya fara zaƙi ko?

Ya fada da sigar tsokana, kamar yadda a Koriya da suke fada bayan an sha bakar wuya, sai kuma ka fara fita daga cikin halin kunci.

"Duk abin da zan sha a yanzu zaki zai min," Lee Si-yeol ya ba shi amsa. Cikakkun 'yan Koriya ta Kudu ba su cika damuwa da Arewa ba, saboda suna ganin Amirka ce za ta damu da wannan.

Amma Si-yeol na gab da fara aikin soji da ya zama wajibi gare shi, a daidai lokacin da zaman tankiya ya yi yawa a yankinsu, ya damu matuka da tsorata.

"Na san ba abu ne da aka saba ba, amma hakan bai dame ni ba lokacin da Kim Jong-un ya harba makamai masu linzami," in ji shi.

"Na damu da sabbin tsauraran matakan da ake dauka ka iya tunzura tashin hankali."

Lee Si-yeol da Lee Geon-ilsu na shakatawa da yammaci gabannin su fara aiki da rundunar sojin kasar

Asalin hoton, BBC/Hosu Lee

Bayanan hoto, Lee Si-yeol da Lee Geon-ilsu na shakatawa da yammaci gabannin su fara aiki da rundunar sojin kasar

Yayin da Farfesa Moon Chung-in ke tsaye ya na kallo ofishin fadar shugaban kasa, ya yi waiwaye kan gazawarsu a fannin diflomasiyya. "Ban hango makoma mai inganci ba,"ya karkare.

"Ban hango wani bau nan kusa ba, ba dai ina raye ba. Wannan damar ta wuce mu."

Farfesa Moon Chung-in ya na shan barasar soju tare da kanwar shugaba Kim Jong-un, Kim Yo-jong, lokacin taron koli na yankinsu

Asalin hoton, Moon Chung-in

Bayanan hoto, Farfesa Moon Chung-in ya na shan barasar soju tare da kanwar shugaba Kim Jong-un, Kim Yo-jong, lokacin taron koli na yankinsu

Akwai rashin tabbas da mutuwar jiki a Seoul, daidai lokacin da Koriya ta Arewa ta ci gaba da gwajin makamai masu linzami, fiye da adadin da sabuwar gwamnatin Koriya ta Kudu ke ganin tsokanar fada ce.

A wani bangaren kuma ana kokarin ganin an sake komawa teburin sulhu kamar yadda kasashen yamma ke fata. Wani tsohon Laftanal Janar din sojin Koriya ta Kudu ya ce "ina kokarin tattara nutsuwata wuri guda."

Duniya ka iya dauke kai, da karkata wani wurin daban, amma bai kamata a manta da tsagerancin Koriya ta Arewa ba.