Wace ce Kim Yo-jong, 'ɓoyayyiyar ƙanwar' shugaban Koriya ta Arewa Kim Jung-un?

Bayanan bidiyo, Wace ce Kim Yo-jong, 'ɓoyayyiyar ƙanwar' shugaban Koriya ta Arewa Kim Jung-un?

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Ƙanwar shugaban ƙasar Koriya ta Arewa Kim Jong-un ta ce Pyongyang za ta mayar da martani da kai harin nukiliya idan har Koriya ta Kudu ta shammace ta ta kai mata hari.

A baya ba a saba jin ta bakin Kim Yo-jong ba, amma a baya-bayan nan ta kasance mai yawan saka baki a kan rikicin da ƙasarta ke yi da maƙwabciyarta.

To me muka sani game da Kim Yo-jong, babbar jami'a a ƙasar, kuma wacce aka yi amannar ita ce mace mai ƙarfin faɗa a ji a Koriya ta Arewa?

Ana bayyana ta a matsayin 'ɓoyayyiyar ƙanwar' shugaban ƙasar.