Pa Sorie: Tunawa da rayuwar sojan Saliyo da ya yaƙi Hitler

Asalin hoton, John Konteh
Samuel Sorie Sesay, daya daga cikin sojojin da suka kusa shudewa daga doron kasa na cikin wadanda suka yi Yakin Duniya na Biyu tare da sojojin Birtaniya, ya mutu a watan jiya a Saliyo yana da shekara 101.
Yayin da ake shirin binne shi ranar Juma'a, Umaru Fofana ya yi waiwaye kan rayuwarsa.
Yana da iya tunawa da abubuwan da suka faru a shekarun baya, sai dai a ganinsa an manta da shi.
Yayin da yake bikin cika shekara 100 da haihuwa a shekarar 2020 tare da iyalansa masu tarin yawa, Pa Sorie - kamar yadda aka fi saninsa - na da batutuwan da yake son yin magana akansu masu yawa.
Ya sanya kayan soja wanda aka jera lambobin yabon da ya samu, jajirtaccen dattijon ya yi magana kan rayuwarsa yayin yakin da yayi a Burma inda yana cikin sojojin da uka yaki na Japan shekara 75 da ta gabata.
Yana cikin sojojin Afirka ta Yamma 90,000 da aka tura zuwa Asiya a wancan lokacin.
An raba su gida biyu da har yanzu ba a cika tunawa da su ko karrama su ba saboda wani yakin na daban. Yakin da ya kusan kai ga a yi galaba kan Birtaniya.
Pa Sorie ya ce Birtaniya ta yi ma sa alkawarin wasu kudade bayan yakin, sai dai har yanzu bai gansu ba.
A kan batun biyan fensho, rundunar sojojin Birtaniya ba ta biyan sojojin da suka yi Yakin Duniya na Biyu, sai idan an raunata su yayin yakin.
Amma wata takarda da ta bayyana a 2019 ta nuna yadda aka rika biyan sojoji 'yan Afirka kudaden da basu kai yawan wanda aka biya takwarorinsu turawa ba.
Sai dai ƙungiyar agaji ta Royal Commonwealth Ex-Services League ta Birtaniya ta taɓa ba shi tallafin wasu kuɗaɗe.

Asalin hoton, IWM/Getty Images
Duk da cewa ba a biya shi ko kwabo ba, amma Pa Sorie ya ce bai yi nadamar shiga soja da yayi ba a 1939, a lokacin shekarunsa na haihuwa ba su kai 20 ba.
Yana iya tunawa da wasu tsofaffin wakokin soja da suka rika rerawa, kuma ya damtse hannunsa yana cewa: "Hitler ayy bongolio!"
Ya ce kalaman na harshen Hindu ne kuma ba zai iya tuna ma'anarsu ba. Sai dai bayyanar sunan Hitler a wakar alama ce ta dalilin da yasa ya shiga yakin.
Pa Sorie ya yi magana kan dakarun Hitler a Burma, duk da cewa abokan gaban nasu sojojin Japan ne ba na Jamus ba.
An fara kai Pa Sorie Legas ne inda aka koya ma sa dabarun yaki a matakin farko - inda ya shiga cikin sojoji daga Najeriya da Gambiya da kuma Gold Coast wato Ghana yayin horon da aka ba su.
Bayan an tura su yankin Asiya, Pa Sorie ya shiga sahun sojojin da suka fafata a yakin Arakan wanda Birtaniya ta yi domin ta kutsa cikin kasar Burma, wadda kasar Japan ta ci da yaki.
Pa Sorie ya tuna da wani yakin da aka yi "bisa wata doguwar gada wadda Japanawa suka so su rusa domin hana mu tsallakawa. Sai dai mun fi karfin su kuma mun tsallaka gadar inda muka kafa sansaninmu cikin daji."
'Ban sake fargaba ba bayan wannan harin'
Sojoji na fuskantar rayuwa mai wahalarwa, inda suke jigilar makamai da kayansu a kansu a cikin dazuka masu duhu da runtsi.
Pa Sorie ya tuna da wani abin da ya faru, bayan da barci ya taba dauke shi yayin yana gadi.
Bayan da ya farka sai yaga wani sojan Birtaniya dauke da wata adda tsaye a kansa kuma yana ikirarin zai kashe shi.
Ya ce daga wannan ranar bai kara yin sakaci a kan aikinsa na soja ba.
"Tun da na tsallake rijiya da baya ban sake fargabar wani abu ba," inji shi yayin da yake murmushi.

Asalin hoton, Getty Images
Bayan da aka kammala yaki, ya kama aikin gwamnati a Saliyo inda aka tura shi ofishin jakadancin kasar da ke tsohuwar tarayyar Soviet.
Sai dai ba a karrama jaruntarsa ba daga wancan lokaci har zuwa lokacin da kasar ta sami 'yancin kai a 1961.
Wannan ne yasa ba a san shi ba sosai a ciki da wajen kasar ta Saliyo.
Amma ganin yadda yake iya takawa a tsaye kyam ba tare da dogara da kwagiri ko sanda ba a shekarunsa da suka kusa kai dari, Pa Sorie ya zama sananne musamman ganin cewa yana cikin sojojin biyu da suka yi yakin Duniya na Biyu da suke da rai a cikin Saliyo.
Pa Sorie mutum ne mai karfin hali. An rika ganinsa yana hawan duwatsun garin Tengbeh a yamma da babban birnin kasar Saliyo wato Freetown, kamar yadda jikansa John Konteh ya shaida.
"Yana da karfin zuciya da kuma juriya, kuma babu shakka wannan halayya ce ta irin jajirtattun mutanen da ya fito cikinsu," inji Mista Konteh.
A wurin da za a binne shi ranar Juma'a, babu shakka iyalan gidan Pa Sorie za su tuna da rawar da ya taka, kuma za su yi fatan wasu ma fara gane dumbin rawar da ya taka tare da takwarorinsa sojojin da suka tafi wata nahiya domin yaki da mutanen da suka so su rikita duniya baki daya.











