Jarabawar Ingilishin da ta rusa rayuwar dubban mutane

.

Asalin hoton, PA Media

    • Marubuci, Daga Ed Main and Richard Watson
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

Wani binciken BBC ya janyo sababbin shakku kan hujjar da aka yi amfani da ita wajen korar dubban mutane daga Birtaniya saboda wai sun yi satar amsa a wata jarabawar nuna kwarewa a harshen Turancin Ingilishi.

Bahasin masu fallasa da wasu takardun hukuma da shirin BBC Newsnight ya samo sun bayyana yadda ma'aikatar harkokin cikin gida ta Birtaniya ke ci gaba da kokarin korar mutane ta hanyar amfani da ikirarin da kungiyar ETS mai shirya jarabawa ta kasa da kasa - duk da cewa ta san akwai shakka mai kwari kan halayyar kungiyar da kurakuren da ke tattare da bayanan da ta ke fitarwa.

An kori mutum fiye da 2,500 kuma akalla an tilasta wa wasu mutum 7,200 daga Birtaniya bayan da kungiyar ETS ta zarge su da satar amsa yayin wata jarabawar da ta shirya. Sauran da aka kyale su ci gaba da zama a cikin Birtaniya kuwa na ci gaba kokarin wanke kansu daga zargin bayan sun shafe shekaru ana muzanta su.

Matakan ladabtarwar da aka dauka bayan wani bincike da shirin BBC Panorama ya yi a 2014 da ya bankado wasu cibiyoyi biyu da ke shirya jarabawar bogi saboda mutane su iya samun damar lashe ta cikin sauki, matakin da zai ba su damar neman izinin zama a Birtaniya.

Bayan wannan binciken ne gwamnati ta bukaci ETS ta binciki girman matsalar satar amsa a cibiyoyi masu zaman kansu fiye da 100 da aka ba kwangilar gudanar da jarabawar.

Bayan wannan umarnin ne ETS ta mika wa gwamnatin wani dogon jadawalin sunayen da ta ce wai sun saci amsa - sai dai duk da cewa an gano sunayen wasu mutanen da ba su aikata laifin komai ba, ma'aikatar harkoki cikin gida ta ci gaba da dogara da hujjar da ETS ta mika mata.

Dan majalisa Stephen Timms daga jam'iyyar Labour ya ce: "A fili take cewa ETS ta tozarta a matsayinta na shaida amma duk da haka ma'aikatar cikin gida na dogara da ita."

BBC ta kuma gano karin hujjoji - wanda ma'aikatar ta dade da saninsu na shekaru masu yawa - wadanda kuma ke kawo shakku kan yada aka amince wa ETS ta binciki abin da ya faru a baya.

A sabon binciken da 'yan jaridan da suka bankado lamarin na farko suka gudanar - BBC na iya bayyana cewa:

  • Ma'aikatan ETS na da da na yanzu sun shaida wa ma'aikatar harkkin cikin gida cewa su gano hujjoji masu kwari na wani shirin satar amsa kusan shekara biyu kafin shirin Panorama ya bankado lamarin
  • Sun shaida wa masu bincike daga ma'aikatar cewa wasu manajojinsu su hana su rufe wasu cibiyoyin, saboda sun damu cewa kudin shigan da suke samu zai ragu
  • Daga wadannan bayanan, ma'aikatar harkoki ciin gida ta gano cewa an boye ma ta gaskiyar girman matsalar
  • An kuma ba masu bincike wasu hujjoji daga wasu wadanda suka shaida yadda aka rika murda jarabawar da wata dabara mai suna "gwaji daga nesa", wadda lauyoyi suka ce tana yi wa hujjojin da ETS ta bayar illa

Shugabar wani kwamitin da ke sa ido kan yadda ake kashe kudaden al'umma na majalisar Birtaniya Meg Hiller ta gaya wa BBC: "Idan aka yi la'akari da abubuwan da ku ka bankado, ina ganin bai dace ma'aikatar harkokin cikin gida ta ci gaba da dogara da bayanai daga ETS ba."

Wahidur Rahman na ciin wadanda suka sha da kyar bayan da ya shafe shekara bakwai yana kokarin wanke kansa daga tuhumar da ma'aikatar harkokin cikin gidan ta yi a kansa, inda ya ce: "Ya kamata su ji kunyar abin da suka yi na kin neman afuwa - ba ma a gare ni ba, har ma ga sauran daliban da basu ji ba, kuma basu gani ba."

An dai fitar da irin wadannan mutanen daga Birtaniya ba tare da an ba su damar kare kansu ba, ba a kuma ba su damar ganin hujjojin da aka yi amfani da su wajen korarsu daga kasar ba.

Ma'aikatar harkoki cikin gida ta soke bizarsu ne ba tare da ta ba su damar daukaka kara ba a Birtaniya.

Nomi Raja na da shekara 22 da haihuwa yayin da ma'aikatan shige da fice suka kai wani samame a gidan da yake haya a matsayinsa na dalibi a shekarar 2014. "Sun nemi in nuna mu su katin shaida na. Sai wani jami'i dauke da rediyon oba-oba ya ce: 'Ya shiga hannu.'"

Sai bayan da aka kai shi wata cibiyar da ake tsare wadanda ake fitarwa daga kasar a filin jirgin saman Gatwick ne wata jami'a ta sanar da shi abin da yasa aka kama shi: "Kawai sai ta ce min, 'Ka rubuta jarabawar Toeic, kuma ka yi satar amsa shi yasa za mu mayar da kai Pakistan'."

Ma'anar kalmar Toeic shi ne: Test of English for International Communication kuma ma'anar sunan jarabawar da ETS ke shiryawa ke nan.

Nomi Raja
Bayanan hoto, Jami'an shige da fice sun kai wani samame gidan da Nomi Raja ke zama

Mista Raja ya yi nasarar dakatar da kokarin fitar da shi daga kasar na kwana 125. Amma kamar sauran mutanen da suka yi kokarin kare kansu daga zrgin satar amsa, hukumomi sun hana shi yin aiki ko halartar makaranta ko ma amfana da tsarin inshora na kasar.

Short presentational grey line

Shirin Panorama na BBC da aka yi a 2014 ya biyo bayan bayanan sirri da wasu suka aika wa BBC cewa akwai daliban da basu san ko kalma daya ta Ingilishi ba da ake "tabbatar musu" cewa za su lashe jarabawar ta Toeic a wasu cibiyoyi biyu.

Sai a fakaice wani mai bincike ya nadi bidiyon wata jarabawa da aka yi a gabashin Landan inda ma'aikatan cibiyar ke ba kowane mai rubuta jarabawar wani mutumin da ya iya Ingilishi wanda an riga an biya shi. Daga nan sai a tura amsoshin zuwa Amurka inda za a duna su kuma a fitar da sakamako.

Bidiyon da Panorama ta dauka na satar amsar da ake yi ya gigita Theresa may, wadda a lokacin ita ce sakatariyar ma'ikatar harkokin cikin gida. "Ina son yin wani abu akan batun," kamar yadda ta ce a wancan lokacin.

Ma'aikatar da ta ke jagoranta ta soke lasisin wasu daruruwan kwalejoji da ke daukar nauyin daliban kasashen waje da ke zuwa Birtaniya, saboda ana tunanin ana amfani da su ne wajen tafka magudi.

Short presentational grey line

Bayan wannan lokaci ne aka mika wa ma'aikatar harkokin cikin gida tarin sunayen wadanda ake tuhuma da satar amsa, kuma ta rika soke bizar duk wanda aka kama da jarabawarsa da aka yi magudi cikinta.

Sai shekarar 2017 ne mutanen da ake tuhuma da wannan laifin suka sami damar daukaka kara a Birtaniya.

A 2016, wato shekara biyu bayan da aka fara fitar da masu wannan matsalar, ETS ta fara mika wa wadanda ake tuhuma da satar amsar sautin jarabawar da suka yi.

Labarin Shakil Rathore ya tayar da tambayoyin da ke neman a amsa su kamar: Shin mutum nawa za su kubuta da an mika musu sautin amsar da suka bayar a jarabawar da aka yi mu su. Sautin ya karyata tuhumar da ake wa mutumin mai shekara 50, cewa ya saci amsa a jarabawar.

Da muka saurari sautin amsar da ya bayar a jarabawar, mun tabatar da muryar ta sa ce saboda yana da wata in'ina da yake yi da ba kasafai ake samun irinta ba. Ya ce: "Lallai wannan muryata ce."

Shakil Rathore and Richard Watson listen back to the recording of Shakil's test
Bayanan hoto, Shakil Rathore da Richard Watson sun saurari sautin amsoshin da ya bayar a jarabawar da aka yi ma sa

Shekara uku Shakil Rathore na kokarin a ba shi wannan sautin. Amma duk da haka sai da ya biya wani kwararren jami'i ya tabbatar muryarsa ce kafin ma'aikatar harkokin cikin gida ta janye tuhumar da ake ma sa.

Wani mutumin kuwa sai da ya shafe shekara shida a wata kotu, inda alkalin ya soki jami'an ma'aikatar saboda gazawar da suka yi na gwada sautin muryoyin nasa da wanda aka nada.

Nomi Raja ya gano kurakurai a bayanan tuhumar da ake ma sa: "An ce ni dan kasar Bangladeshi. Amma daga Pakistan nake. An kuma ce a wata cibiya da ke Leicester na rubuta jarabawar, amma a Landan na rubuta tawa jarabawar."

Bayan shekara biyar da aka saurari karar da ya daukaka, inda alkalin ya ce, "bai aikata wani laifi ba."

Short presentational grey line

A 2018, kamfanin ETS Global BV ya biya ma'aikatar harkokin cikin gida ta Birtaniya fam miliyan 1.6, sai dai kafin lokacin badakkalar ta janyo wa gwamnatin kasar asarar fam miliyan 21.

An kuma yanke wa mutum 21 da aka kama da laifin satar amsa hukunci, ciki har da mutum 11 da shirin Panorama na BBC ya nada a bidiyon sirrin nan da ya haifar da bincike mai zurfi kan batun.

Gwamnatin kasar kuma na ci gaba da dage wa cewa ta yi daidai kan matakan fitar da dubban mutanen da sakamakon ETS ya ce sun yi satar amsa daga kasar.

Zuwa 2019, fiye da mutum 3,700 sun yi nasara a karar da suka shigar a kotunan Birtaniya.

A watan Fabrairun 2021, sakatariyar harkokin cikin gida Priti Patel ta gaya wa 'yan majalisa cewa lallai akwai wadanda aka tuhuma da ba su aikata wani laifi ba. "Muna bukatar gano maslaha ba karin haske kawai ba, lallai muna bukatar a yi adalci kan wannan batun."

Ta yi alkawarin sake duba wasu hanyoyin kaucewa sake aukuwar wannan badakkalar, amma shekara guda bayan yin alkawarin, babu wani mataki da aka dauka.

Kuma har yau ma'aikatar harkokin cikin gida ta Birtaniya ba ta yarda cewa akwai kurakurai masu girma a shaidar da ETS ta gabatar ma ta ba.

Ma'aikatar ta kara da cewa ta inganta tsarin ta yadda ba za a sake tafka magudi irin na baya ba.